Maraici da mutuwar aurena ne suka buɗe tunanina kan kafa gidauniya  – Mariya Durumin Iya 

Spread the love

“Mace na rayuwa ne ƙarƙashin kulawar wasu har ƙarshen rayuwarta”

Daga AISHA ASAS 

Rayuwar aure rai ne da ita tamkar dai yadda aka san ɗan adam da ruhinsa, yayin da mai shar’antawa Ya yi kira, ruhinsa ba zai ƙara ko sa’a ɗaya a jikin ba, zai fice yana mai amsa kiran mahallici. Idan kuwa ba shi ya yi kiran nasa ba, ko duniya za ta taru don ganin ta tsayar da numfashinsa ba za ta iya tsayar da shi ba.

Haka ita ma rabuwar aure, daga auren har ranar ƙarewar sa rubatacce ne, idan ranar rabuwa ta zo, ko da tsananin soyayya sai kaga an rabu, haka idan bai hukunta za a rabu ba, duk rikicin aure sai ki ga ya yi ƙarko. 

Duk da wannan sani da muke da shi, a ƙasar Hausa, ana yi wa matan da auren su ya mutu mummunan fahimta, yayin da wasu ke shiga garari sakamakon zawarci.

Shafin Gimbiya na wannan mako ya samu baƙuncin jajirtacciyar mace, da ke fafutukar wayar da kan al’umma tare da nusar da su muhimmancin tallafa wa matan da aurensu ya mutu, da waɗanda mazajensu suka mutu, ga kuma uwa uba tarbiyya da ta ke koyarwa ga iyaye mata.

Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Mariya Inuwa Durumin Iya:

MANHAJA: Sunanki sananne ne, don haka tarihin rayuwarki ne muradin masu karatunmu.

MARIYA DURUMIN IYA: Assalamu alaikum. To kamar yadda yake maƙale jikin sunana, an haife ni a Unguwar Durumi Lokon Iya Marafa, kuma na yi karatu na addini da na zamani. Na yi karatun Al’ƙur’ani a nan unguwar ta Durumin Iya, makarantar allo, kuma a nan ne na yi saukar Al’ƙur’ani, Ina da shekaru 14, a makarantar Malam ɗanjummai.

Bayan kammala saukar na ɗora da karatun littafai, daga nan har zuwa makarantar dare da nake zuwa. Alhamdu lillah, karatun addini an same shi daidai gwargwado, saboda ko karatun nawa na bokon ma na yi shi ne a ɓangaren addini.

Na yi makarantar firamare a Guma Primary School, sannan na ƙarasa a Gidan Galadima. Sai kuma makarantar gaba da firamare da na yi ta a ‘Kuliyyattul Tarazzul Islam’ Gwarzon Dutse. Makaranta ce da marigayi Sheikh Nasir Kabara ya yi. To alhamdu lillah, na san daga cikin sunan ma za a fahimci ta ilimin addini ce.

Bayan nan kuma na yi karatu a ɓangaren shari’ar Musulunci, wato Islamic Law, a Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies. Sannan na yi karatun ‘Education’ a ‘Islamic Studies a matsayin digiri na na farko, a Jami’ar Maitama Sule. Sai kuma digiri na biyu wanda nake kai yanzu a Jami’ar Bayero, shi ma dai akan ‘Education’ ɗin ne, amma a ɓangaren ‘Adult and Non-formal Education’. Wannan shi ne abinda ya shafi ɓangaren karatu kenan.

A ɓangaren rayuwa, alhamdu lillah, Ina da aure, kuma Ina zaune da maigidana lafiya. Sannan mahaifina ya rasu tun ban fi shekaru 16 ba. Ina tare da mahaifiyata da ‘yan’uwana. Alhamdu lillah. Ina ‘yan ƙananan kasuwanci namu na mata, sannan Ina gudanar da aikin gidauniya ta.

Kin kasance ɗaya daga cikin jajirtattun matan Arewa da ke fafutukar nema wa ‘yan’uwansu sasauci kan raɗaɗin talauci, ta hanyar samar masu da ababen buƙatu. Za mu so jin yadda wannan tunanin naki ya samo asali.

To alhamdu lillah. Wato ni har kullum Ina kallon kowacce matsala ta mata, na kan yi ƙoƙarin ganin na zurfafa tunani kan wai mai ya janyo matsalar ne? Menene asalin abinda ya janyo fatuwar matsalar koma wacce iri ce. Ba ma ta mata ba kawai, domin duk matsalar da aka ga ta faru, to kamata ya yi a maida hankali akan gano ainahin menene matsalar, me ya jawo ta.

To, ni nawa tunanin akan ‘yan’uwana mata ya samo asali ne kamar yadda na faɗa a baya ni marauniya ce. Na fara rayuwar maraici tun shekara ɗaya bayan kammala karatun sakandire. Kuma ni ce ƙarama a gidan. To gaskiya ga wanda ya san yadda rayuwa da mahaifa ta ke, yadda maraici yake, ya san idan aka ce mutum ya rasa mahaifinsa tun ma a ce bai ma wani girma sosai ba, giɓi ne mai girma.

Bayan nan kuma sai na zo na yi aure, sai muka rabu da maigidana, to wannan rabuwar auren nawa ta sa tunanina ya daɗa buɗewa kan ababen da suka shafi rayuwar mata a lokacin da ta rasa iyayenta da kuma yadda take rayuwa a lokacin da ba ta da miji. Yadda mace take rayuwa a irin wannan lokaci kusan za a ce ba ta da gata. Duk da cewa, a ɓangare na ni bazan ce na yi rayuwa ta rashin gata ba, don ban bari zuciyata ta mutu ba, asalima ban taɓa yarda na amince cewa, ba ni da gata ba, domin idan har ka amince ubagijin ka na nan, kana da ranka da lafiyarka, to ba za ka kira kanka marar gata ba.

To, tun daga wannan lokacin da hakan ta kasance gare ni, sai nake tausayin mata, tare da yi masu uzuri kan wasu ababe, sannan na kan fahimci inda matsalar su ta samo asali yayin da suka bayyana min ita. Shin irin tawa ce, wato auren ta ne ya mutu, ko mijinta ne ya mutu, kuma dangin nasa ba su karɓi ɗawainiyar ta ko ta ‘ya’yanta ba, koko da auren ta ya mutu ta dawo gida, iyayenta ba su karɓi ɗawainiyar ta, tana da sana’a, tana aiki ne, yaya ta ke gudanar da rayuwarta? Ire-iren waɗannan tunanin ne ya sa na hango buƙatar wayar da kai ga matan. A dinga tunantar da mu rayuwa, kar mace ta ɗauka cewa, idan auren ta ya mutu, ko mijinta ya mutu, ko idan ba ta samu miji ba, ko ba ta yi aure da wuri ba, kamar shi kenan rayuwarta ta zo ƙarshe. 

A’a. Akwai gudunmawa da yawa da za ta iya ba wa kanta da kuma al’umma koda ba ta da aure. Shi aure ƙaddara ce da Allah ne mai hukunta wanzuwar sa ko akasin hakan, kuma rashin samuwar sa a kanki ba yana nufin kin yi wa Allah laifi ko ba Ya son ki ba, domin akwai bayin Allah mata da dama da muka ji tarihinsu da wasu darajarsu mai yawa ce da annabta ne kawai ba a ba su ba, amma sun yi rayuwarsu ba tare da an ƙaddara masu aure ba.

To kinga idan muna kallon irin waɗannan za mu ga lallai akwai gudunmawar da mata za su iya bayarwa a cikin al’umma wadda ba lallai sai tana gidan miji ba, ko sai ta rayu rayuwar jin daɗi, irin a ce, tana da miji, tana da uba ba, a’a. Kowacce mace akwai irin baiwar da Allah Ya yi mata, wadda idan ta tsayu akan ta, ta jajirce, za ta more kanta, wasu ɗin ma za su more ta.

To wannan ne dalilin da ya sa na ce, kar na kashe zuciyata, bari na yi, wataƙila daga ni, wasu matan ma za su kwaikwaya, su jajirce akan kansu don su inganta rayuwarsu.

A matsayinki ta mai jan ragamar Gidauniyar Wayar da Kai da Cigaban Al’umma, (Foundation for Social Orientation and Gender Deɓelopment). Za mu so sanin yadda wannan gidauniyar ta soma.

To alhamdu lillah. Gidauniyar Wayar da Kai da Cigaban Al’umma, wato ‘Foundation for Social Orientation and Gender Deɓelopment’, ta kafu shekaru uku da suka wuce, ranar 18 ga watan Disamba, shekara ta 2020. Ita ce ranar da na karɓi satifiket ɗin ta daga CAC, don haka nake ɗaukar wannan rana a matsayin ranar da gidauniyar ta kafu. Kuma alhamdu lillah, wannan gidauniyar ta samo asali ne daga wancan tunanin nawa, na yaya zan taimaki mata ‘yan’uwana, waɗanda suka samu kansu a irin rayuwar da na samu kaina a ciki.

Yawanci za ki ga idan aka ce mace aurenta ya mutu, ko mijinta ya mutu, kallon farko da mutane ke yi mata shi ne, wannan macen zaman kanta ta ke yi, musamman wadda ta ke fita ta nemi halalin ta, ta ke fafutar neman na rufa wa kai asiri, ta ke ‘yan kasuwancinta haka, saye dai da siyarwa, ko kuma tana aiki, sai a ɗauka wannan macen zaman kanta ta ke yi, ta fi ƙarfin kowa, ba ta son zaman aure, ba ta da haƙuri, ta zaɓi wata rayuwa marar kyau. To kuma idan ta zo ta zauna ɗin, ba ta da auren, kuma ba ta komai, ba fa wanda zai ɗau nauyin nata, ba wanda zai ɗauke mata buƙatunta, tunda dai shi mijin ya riga ya sake ta. Hakan na nufin idan ta zauna ɗin ciwon damuwa ne zai kamata ko Ire-iren curutan nan da ƙuncin rayuwa zai iya janyowa.

To a lokacin da na gama digiri ɗina na farko, muna zaman jiran sakamakon, sai ya zama an faɗa yajin aiki. Wannan tafiya yajin aikin da aka yi, ya taɓa ni ƙwarai da gaske, domin zaƙuwa da muke yi na ganin sakamakon, don ka ga ka ci ko ba ka ci ba. Yajin aikin dai ya ɗauki tsayin watanni 8, don haka a wannan lokacin ne na yi tunanin Ina ta zaune a gida, tunda ba na aiki, Ina tambayar kaina me zan yi?

To sai na yi duba da rayuwar da na yi a jami’a, na fahimci abubuwa da yawa na lalacewar tarbiyya, wanda a lokacinmu ba haka suke ba, domin a lokacin da na yi difloma ne na yi aure, sai kuma muka rabu da mijina, sannan na sake komawa karatun, wato digiri ɗina na farkon. To a wannan lokacin da na kalli yadda rayuwar mata ta zama a jami’a da abubuwan da ake yi a ciki, sai na ke mamaki, yaushe al’ummarmu ta zama haka ne? Yaushe lalacewar tarbiyyarmu ta zama haka? 

To bayan mun gama karatun, mun tafi wannan yajin aikin, sai na fara tunanin yadda zan iya bayar da tawa gudunmawar. To a nan ne tunanin yin rubutu kan tarbiyyar mata ta zo min, wataƙila koda ni ban mora ba, tunda ba ni da ‘ya ko ɗan da zan yi wa tarbiyya yadda ni ma aka yi min, idan na bari a rubuce, wata rana wasu za su duba, kuma zai amfane su a tarbiyyar nasu ‘ya’yan. Kinga kuwa zan samu wannan lada.

Da wannan na fara rubutu, wanda har ya kai ni ga rubuta littattafai guda uku; ɗaya akan almajiranci ne mai suna ‘Almajiranci da Bara’, sai kuma wanda na yi akan tarbiyya mai suna ‘Rayuwar Mace daga Haihuwa zuwa Tsufa’, sai kuma ‘Soyayya da Rayuwar Aure a ƙasar Hausa’ wanda shi ma ya shafi tarbiyya, amma akan abinda ya shafi zamantakewar aure. 

To bayan na kammala waɗannan littattafan, aka yi bikin ƙaddamar da su, sai kuma tunanin kafa wannan gidauniyar ya zo min. A lokacin akwai wani wanda baba ne a wurina, ya ce, tunda wannan damar ta samu, domin a lokacin alhamdu lillah an fara gayyata ta gidajen rediyo da na talbijin, yin shirye-shiryen da suka shafi tarbiyya, da wanda ya shafi wayar da kai, zamanantar aure, to shi ne fa ya ce, me zai hana mu yi abinda zai ba wa mutane dama su iso gare mu da matsalolinsu, ta yadda za a iya samun mu kai tsaye, a yi magana da mu, a tattauna, wataƙila hakan zai sa a samu mafita.

To da wannan shawarar na duba, a matsayina ta ɗalibar shari’a, duk abinda zan yi na fi son in yi shi bisa tsari da kuma ƙa’ida, don haka sai na ce bari na yi abinda zai kasance na samarwa kaina aikin yi kuma har na samar wa wasu. To da wannan ne wannan tafiya ta fara, wadda nake fatan ko bayan raina, ko kuma idan aka wayi gari ni na dena, wasu su tallafe ta, su ci gaba da yi. Saboda ba mai burin ya asassa wani alheri a ce ya tsaya.

Zuwa yanzu kuma ba abinda za mu ce sai alhamdu lillah, domin cikin ababen da muke yi akwai taruka na wayar da kai akan wasu matsaloli, musamman ma abinda ya shafi tarbiyya da zamantakewar iyali. Tunda shi ne babban jigon mace, a bata tarbiyya, ita ma ta bayar, ta kula da iyali. Duk wani da aka gan shi abin sha’awa a duniya to mace ce ta mayar da shi hakan. Akasin haka ma za mu iya cewa daga macen ne.

Fatanmu rayuwar mata ta inganta, su zama abin sha’awa, a daina yi wa mace marar aure mumunan fahimta, a ba su dama su ma a ga nasu kamun kan, wanda wataƙila wata ta fi ma mai auren kamun kai.

Menene ayyukan wannan gidauniyar?

Gidauniyar na da ayyuka masu yawa, masu faɗi, duk da dai mun taƙaita su, to amma manya-manyan ayyukanmu akwai kula da iyayen marayu. Mu kan taimaka masu da jarin yin sana’a, ko kuma idan suna da sana’a, mu taimaka masu da abinda zai ƙara bunƙasa sana’arsu. Wani lokacin kuma mukan taimaka wa yaran ta ɓangaren biyan kuɗin makaranta da dai ɗawainiyar karatu. Sannan mukan ɗauki nauyin yara mata, a koya masu hanyar dogaro da kai, kamar koyon na’ura mai ƙwaƙwalwa. Sannan a cikin ayyukan mu akwai taimaka wa marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi. Sannan akwai bada shawarwari kamar yadda na faɗa, sulhu a auren ko kuma masu shirin yin auren. Kuma mukan shirya tarukan wayar da kai, musamman ma ga ‘yanmata.

A matsayinki ta mace, ko kin fuskanci wani ƙalubale a lokacin da ki ka yi yunƙurin asassa wannan abin alherin?

Eh, ai kamar yadda na gaya miki, a ‘society’ mu, ana ganin duk macen da ba ta yi aure ba, ana mata kallon marar haƙuri, ko mai zaman kanta, fitinanniya dai haka wadda ba ta jin magana. To gaskiya a lokacin da na yi shirin yin wannan gidauniyar na fuskanci matsala, a ɓangaren ‘yan’uwana da na yi ta neman shawarar su, kuma na so su zo mu haɗa hannu muyi aikin nan a tare. To alhamdu lillah dai abin ba wani nisa ya yi ba duk suka fahimce ni. ƙalubale na biyu da muka fuskanta shi ne, bayan yi wa gidauniyar rijista muka yi ta fafutukar neman inda za mu zauna, wato ofis kenan, saboda aiki irin wannan muna buƙatar wurin zama ni da abokan aiki. To sai ya zama idan muna son yin wani metin haka a lokacin sai dai mu samu kamar wurin cin abinci, mu zauna, a tattauna. To wannan ma ba a wani daɗewa ba ya wuce.

Sai kuma ƙalubale na yadda aka yi ta kallon cewa ba zan yi aure ba tunda na shiga wani abu, wanda ake cewa yawancin masu yin sa mata ne da suka gagara, ko ba sa jin magana, zan fara yawon garuruwa da sauransu. To yanzu dai alhamdu lillah na yi auren, kuma Ina zaune lafiya da maigidana, kuma Ina cigaba da ayyukan gidauniyar. Waɗannan ne ƙalubalen da suka zo suka wuce. Masu zuwa a nan gaba kuwa, in sha Allahu mun sha ɗamarar ɗaukar su.

Za mu ci gaba

By ukarofi