Kafin a yaba da gudunmawar mace sai ta yi abin da namiji yake yi sau goma – Aisha Lawal 

Spread the love

Ni ce a karan kaina na yi tunanin ƙirƙiro da shirin Mata A Yau

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Ga duk wani ma’abocin kallon tashar talabijin ta Arewa 24 ba zai kasa sanin, ɗaya daga cikin shugabannin tashar ba, mai tsarawa da gabatar da shirye-shirye daban-daban, irin su Mata A Yau, da Zamantakewa, wato Hajiya Aisha Lawal Umar. A wannan makon za mu kawo muku wata tattaunawa da wakilinmu Abba Abubakar Yakubu,  ya yi da wannan ƙwararriyar ma’aikaciya, wacce ta kasance ɗaya daga cikin fitattun mata ýan jarida na Arewa, kuma abin koyi ga matasa da ýan mata ýan jarida masu tasowa. A sha karatu lafiya.

MANHAJA:  Da farko za ki gabatar da kan ki.

AISHA LAWAL: Sunana Aisha Lawal Umar. Ni ýar jarida ce, matar aure, kuma uwa. Ni ‘yar asalin Jihar Bauchi ce daga wani gari da ake ce wa Udubo a ƙaramar Hukumar Gamawa.

Za mu so mu ji wani abu daga tarihin rayuwarki.

An haife ni a garin Bauchi,  kuma na yi karatuna na firamare har zuwa sakandire a cikin garin Bauchi, daga bisani kuma na wuce Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, inda na yi digiri na farko da na biyu dukka a fannin aikin jarida wato Mass Communication. Na gama a shekarar 2010. Bayan na kammala aikin hidimar ƙasa sai na fara aikin a  tashar AIT dake Bauchi, daga bisani kuma da na yi aure sai na dawo Kano da zama, inda na fara aiki da tashar talabijin ta Arewa24.

Ba mu labarin yadda ƙuruciyarki ta kasance, wacce tarbiyya ki ka samu yayin tasowarki?

Alhamdulillah, mun samu tarbiyya sosai daga wajen iyayenmu. Mamana ta kasance uwa mai lura sosai da tsanani wajen tarbiyya. Ba a bar mu sakaka mun yi abin da muke so ba a lokacin tasowarmu, muna ganin kamar takurawa ce, sai yanzu na gane ashe taimako ne ba kaɗan ba aka yi mana.

Me ya ja hankalin ki zuwa ga aikin jarida? Shin tun farko dama shi ne aikin da ki ke sha’awar ki yi?

Akwai wani kawuna wanda ya kasance ɗan jarida ne sosai, ya taɓa zama Shugaban tashar talabijin ta BATɓ a Bauchi, wacce take ƙarƙashin gwamnatin Jihar Bauchi, Ukasha Umar Udubo. Shi ne ya fara sa mini sha’awar aikin jarida, da sanin muhimmancin ýan jarida a cikin al’umma. Kodayake ba aikin jarida naso in yi ba da farko, a lokacin ra’ayina ya fi karkata kan aikin lauya. Sai dai lokacin da na yi jarrabawar neman shiga jami’a, na nemi damar yin karatun lauya a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a 2003 ban samu ba, saboda makin da na samu bai kai wanda ake nema ba, don haka sai aka bani  damar nazarin aikin jarida. Ka ji yadda aka yi na samu kaina a wannan layin, kuma Alhamdulillah ban yi nadamar karatun da na yi ba, ko aikin da nake yi a halin yanzu.

Wacce gudunmawa ki ka samu daga gida, wanda ya taimaka miki wajen cimma burinki na rayuwa?

E, Kamar yadda na faɗa a baya, kawunai na, Ukasha Umar Udubo da Ibrahim Umar Udubo, sun taka muhimmiyar rawa wajen dasa min ƙaunar aikin jarida a raina, tun a matakin farko. Sannan sun kasance suna bani ƙwarin gwiwa sosai. Don ko a lokacin da na samu aiki a AIT Abuja, naso na ƙi zuwa, shi wannan kawunan nawa Ukasha shi ne ya dage lallai sai na je, kuma ya taimaka min don ganin na kwantar da hankalina na yi aikin. A gaskiya waɗannan dalilai su ne suka bani ƙwarin gwiwa a aikin jarida. 

Kina ganin kwalliya tana biyan kuɗin sabulu kuwa, lura da irin darussan da ku ke tattaunawa a kansu cikin shirin ‘Mata A Yau’?

Alhamdulllah, mukan samu ƙalubale sosai, amma dai gaskiya tabbas kwalliya tana biyan kuɗin sabulu. Mu burinmu mata su san kansu, kuma su kasance masu neman na kansu. Ka da su ce komai sai an musu, yanzu rayuwar aure tana buƙatar taimakekeniya. Kuma Alhamdulillahi ta wannan shirin mata sun koyi sana’o’i da yawa, sun ji daga bakin mata ‘yan’uwansu waɗanda suke sana’o’i daban-daban, ƙalubalensu da kuma nasarorinsu. Duk manufar ita ce su koya daga ‘yan’uwansu mata.

Ko za ki gaya mana gwagwarmayar da ku ke sha yayin shirya shirin ki na ‘Mata A Yau’?

A gaskiya ni mace ce mai burin ganin na samar da canji a rayuwar mata, duk da kasancewar dama na daɗe ina gabatar da shirin Zamantakewa, amma a cikin zuciyata ina da burin ganin na samar da wani shiri da zai zama kamar majalisar mata, inda daga matakai daban-daban za su riƙa tattaunawa da ba da shawarwari kan rayuwar mata. Naso a ce shirin ya samu mata kamar shida da za su riƙa jagorantar shirin, amma sai ya kasance huɗu aka iya samu. Sannan ni ba na so in zama daga cikin masu gabatarwa, na fitar son in kasance daga waje, ina nazarin abubuwan da ake tattaunawa da hanyoyin da za a warware su. Amma a gaskiya akwai ƙalubale  sosai. An zage mu, an ce mana Yahudawa,  da dai sauransu. Babu abin da ba a faɗa ba. Allah Ya sani ni ce a karan kaina na yi tunanin ƙirƙiro da shirin, kuma na tsara shi ta yadda za a wayar da kan matan Arewa, su fahimci yadda rayuwa take tafiya, kuma nunawa duniya irin gudunmawar da suke bayarwa, a fannonin rayuwa daban-daban. Kuma Alhamdulillah, shirin yana cimma burinsa, domin akasari matan da muke kawowa su baƙunci shirin Mata A Yau,  fitattun mata ne da duniya ta shaida irin gudunmawar su da rawar da suke takawa a siyasance, a kimiyya, a kiwon lafiya, a kasuwanci, da ayyuka daban-daban.

Akwai lokacin da su masu gabatarwa suke kasa fahimtar wasu abubuwan, saboda yadda masu kallo suke aibata su ko munana musu zato. Alhalin a bayan fage ni ce mai ƙirƙiro da maudu’in da za a tattauna akai da ba da shawarwari kan yadda tattaunawar za ta tafi. Su masu kallo ba su san da haka ba, masu gabatar da shirin suka sani. Don haka idan sun tashi zagi ko faɗar ra’ayinsu kai tsaye su za su zarga. Na fuskanci ƙalubale sosai,  ba daga abokan aikina ba, ba daga masu kallo ba. Akwai ma wasu dake cewa shirin zai jawo a rufe tashar Arewa 24 bakiɗaya, saboda yadda mutane a waje suke fusata kan wasu abubuwan da ake tattaunawa a cikin shirin.

Wacce shawara ki ke bai wa yara mata da suke nuna sha’awar aikin jarida, sakamakon yadda suke ganin ayyukan ki a Arewa 24?

Kullum ina gayawa yara dake tasowa cewa, aikin jarida ba na rago ba ne, sai kin jajirce sosai. Saboda a aikin jarida kafin a yaba da gudummawar mace sai kin yi abin da namiji yake yi sau goma, kafin a fahimci ƙoƙarin ki. Domin a matsayin mu na mata muna da rauni, kuma akwai nauye-nauye daban-daban dake kanmu, za ki kula da gida, za ki kula da maigida, za ki kula da yara, ga shi nan dai. Shi ya sa nake gayawa mata, in har kin ɗauki jakarki kin ce kin fita aiki ko wajen wata ssana’a kina mace to, gaskiya ba kya buƙatar a tausaya miki, ko a ɗaga miki ƙafa, domin da kin fara kawo uzurori don ke mace ce to, babu inda za ki je. Dole ne ki zama jajirtacciya, ki yi da gaske, iyakar iyawarki, don ki samu cimma nasara. E, za ki iya samun ciki ko rashin lafiya a yayin aikin, amma in ki ka tsara komai, za ki samu komai da sauƙi. Amma in ki ka fara nuna ƙyuya da yawan kawo uzurori don a tausaya miki to, babu inda za ki je. 

Akwai lokacin da ke da kan ki in an ce ki huta ba za ki so ba, musamman idan kina matakin jagorantar wasu mutane. Domin in har ke baki tsaya kin yi ba, sauran na ƙasa da ke ma ba za su yi ba. Dole ki nuna kyakkyawan misali.

Abu na biyu kuma, idan ki ka samu miji ko iyaye da suka yarda da ke to, dole ne ki tabbatar da wannan amincewar da aka nuna miki. Amma da zarar kin fara nuna shiririta da rashin mayar da hankali har aka gano ki a haka to, babu mai yarda ya baki wata dama. Dole ne ki nuna da gaske aikin za ki yi, kuma ba ki bari wani abu ya kashe miki ƙwarin gwiwar ki ba, ko wani ya janye hankalinki zuwa ga wani abin shirmen daban ba. Ta haka ne a gida za ki samu amincewar iyayenki, ko maigidanki, hatta a wajen aiki za a riƙa mutunta ki, saboda ba ki ba da ƙofar da za a raina ki ba.

Me ya fi burgeki a aikin jarida?

Abin da ya fi burge ni da aikin jarida shi ne, za ka yi wa dubban jama’a magana ka isar musu da saƙo ba tare da kun taɓa haɗuwa ko ka san su sun sanka ba. Za ka isar da saƙon gyara kayanka,  ba sai ka tara jama’a a zahiri ko ka hau minbari ba. Daga inda ka je gabatar da shirye-shiryenka, ko rubuce-rubucenka, za ka isar da saƙo ga masu karatu ko sauraronka,  kuma har a yi sa’a, wasu su ɗauki darasi daga abin da ka ke isar musu. Gaskiya wannan abin yana burgeni sosai. 

Wanne ƙalubale ki ka fi fuskanta a yanayin aikin da ki ke yi?

Ku biyo mu a mako mai zuwa don samun amsar wannan tambaya tare da wasu tambayoyin waɗanda muke fatan mai karatu zai gamsu da su.

By ukarofi