
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya yi kira da a samar da sulhu a tsakanin jagororin siyasar Benuwai, yana mai gargaɗin rashin jituwa tsakanin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Sanata George Akume da Gwamna Hycint Alia na jihar ka iya haifar da babban ƙalubale ga jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Da yake jawabi a taron ɗaurin auren ɗan Akume da wata mai suna Deborah da aka yi Makurɗi, Shettima ya jinjina wa tarihin Benuwai wajen inganta haɗin kan ƙasa.
Ya tunatar da yadda a tsawon shekaru da suka gabata, wani ɗan Borno da ya rasa muhallinsa ya samu matsuguni a garin Jemgbagh na Benuwai, inda daga bisani ya zama ɗan majalisar dokoki ta tarayya a tsakanin 1961 da 1965.
Ya ce, Benuwai ita ce “bugun zuciyar ƙasa” kasancewar al’ummar ƙabilar Tibi sun mamaye yankunan jihar, Taraba, Nasarawa, Abuja, Kogi da wasu sassan Borno.
Ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa ga yadda suka yi wa Shugaba Bola Tinubu ruwan ƙuri’u a zaɓen 2023 duk da cewa ba ɗan addini ko ƙabilarsu ba ne, yana mai bayyana jihar a matsayin jagora a Arewa ta Tsakiyar Nijeriya kuma ginshiƙin haɗin kan ƙasa.
Shettima ya kuma yaba wa daɗaɗɗen zangon siyasar Akume inda ya bayyana shi a matsayin “mage mai rai tara” wanda ya riƙe muƙaman darakta, babban sakatare, gwamna, sanata, jagoran marasa rinjaye, minista a yanzu kuma SGF.
A nasa jawabin, Sanata Akume ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa karrama taron ta hanyar halartar mataimakinsa.
Shi ma Gwamna Alia, a saƙonsa na fatan alheri ya jaddada muhimmancin haɗin kai da taimakekeniya tsakanin iyalai da jagorori, yana mai taya ango da amarya murnar shiga sabon rayuwa gami da addu’o’in samun albarka acikin sa.
