2027: Peter Obi na shirin sanar da komawarsa ADC a hukumance

Spread the love

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, na ya kammala shirinsa na shiga jam’iyyar ADC gabanin babban zaɓen shekarar 2027 bayn shawarwari da abokan siyasarsa.

Wata majiya a jam’iyyar ta shaida cewa Obi ya kammala shirye-shiryen shiga ADC tare da gudanar da taron bayyana matsayinsa a Inugu ranar 31 ga Disamba, yayin da magoya bayansa suka fara shirye-shiryen sauya sheƙa.

Rahotanni sun bayyana cewa, ya kuma gana da Shugaban ADC na ƙasa, David Mark, domin sabunta goyon baya ga haɗakar jam’iyyar.

Saidai Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce babu sanarwa a hukumance tukuna, duk da cewa tattaunawa na gudana. Haka kuma, tafiyar ‘Obidient Movement’ ta ce Obi ne kaɗai zai iya yin bayani akan lamarin.

A halin da ake ciki, ADC ta sanar da shirin gudanar da taron ƙasa a tsakiyar 2026 domin sake tsara jam’iyyar da kuma fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.

Ta kuma ce za ta mayar da hankali kan faɗaɗa membobinta da ƙarfafa tsarinta a faɗin ƙasa, tare da shirya taruka biyu a 2026 na amincewa da shawarwarin majalisar zartarwar (NEC) da kuma zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.

By Babaji