Gwamnonin APC za su kai 29 yayin da Abba Kabir Yusuf na Kano ke shirin koma wa jam’iyyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa mai mulki, wato APC.

A cewar rahotanni, za a aiwatar da hakan ne a ranar 6 ga watan Junairu, 2026 ko da sanya albarka daga mai gidansa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ko kuma akasin haka.

Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya yanke shawarar haka ne bayan tattaunawa da neman shawarwarin masu ruwa da tsaki a jihar ciki har da mambobin majalisar dokokin jihar, ciyamomim ƙananan hukumomi da wasu ƴan majalisar tarayya da ke wakiltar yankunan Kano.

Wannan al’amari ya janyo hankalin jama’a musamman yadda a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen watsa labarai a jiya Lahadi aka ga Daraktan harkokin gwamnatin gwamnan, Abdullahi Ibrahim Rogo yana bayyana goyon bayansa a fili akan komawar Abba APC.

Da yake jawabi a wajen jagororin jam’iyyar a Ƙaramar Hukumar Rogo, Ibrahim Rogo ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki a yankin sun cimma bin sawon gwamnan duk inda ya koma a fagen siyasa.

Ya bayyana cewa, komawa APC ga gwamnan shi ne abin da ƴan jihar suke so Nijeriya, da ma shi kansa Kwankwaso, yana mai ƙarawa da cewa jam’iyya mai mulkin ta samar da fagen siyasa mai ƙarfi a faɗin ƙasar.

Abba Kabir Yusuf shi ne kaɗai zaɓaɓɓen gwamna daga jam’iyyar NNPP a babban zaɓen 2023.

Haka kuma sauya sheƙar tasa za ta sanya adadin gwamnonin APC ya kai 29. Tun daga 2023 zuwa yanzu, APC ta samu ƙarin gwamnoni guda bakwai daga jam’iyyun adawa musamman PDP.

By Babaji