
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin (mai ritaya) ya bayyana yadda ubangiji ya taimaka shi a zangon jagorancinsa a matakin ƙasa, inda ya ce ɗaukakarsa ta samu ne yayin da yake tsaka da fuskantar ƙalubalen makirce-makircen maƙiya na ƙoƙarin kai shi ƙasa.
Janar Musa ya faɗi haka ne a jiya Lahadi a Cocin Conquerors Global Assembly da ke Abuja, inda ya je bauta tare da iyalinsa.
Da yake godiya ga mahaliccinsa, Ministan tsaron ya ce tawakkali da juriya su ne silar nasararsa, yana mai cewa ɗan-adam ba zai taɓa iya ja da ƙaddarar ubangiji ba.
Ya kuma yi godiya ga wanda ya samar da cocin, wato Bishop David Abioye da matarsa, wanda ya bayyana a matsayin na hannnu dama a gare shi.
Ministan ya yi addu’ar cigaba da samun nasara ga cocin, yana mai kira ga masu bauta da su kasance masu tawakkali a yayin fuskantar ƙalubalen rayuwa.
Tsohon babban hafsan tsaron Nijeriyar, ya kuma ƙarfafa wa al’ummar Nijeriya da cewa kada su karaya ko deɓe tsammani daga samun nasara, yana mai cewa cika alƙawarin ubangiji abu ne na tabbas da ba a iya hana faruwarsa.
A ranar 2 ga watan Disamba Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Janar Musa a matsayin Ministan Tsaro, kwanaki biyu bayan Mohammed Badaru ya sauka daga muƙamin akan abin da ya kira da dalilai da suka shafi lafiyarsa.
