DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya
Wani mummunan hatsari ya auku a jiya Lahadi 28 ga watan Disambar shekarar 2025 da ake ciki da yamma inda wasu manyan tirela gudu uku suka ƙwace daga babban titi suka auka wa wasu mutane a lokacin da ake wani babban bikin al’adar ƙabilar Eggon wadda ake gudanar a ƙarshen shekara-shekara mai taken “Ame Wo Ba Eggon cikin harshen na Eggon.
Lamarin ya auku ne a garin Nasarawa-Eggon a Jihar Nasarawa inda lamarin ya laƙume rayukan mutane biyar nan take tare da raunana dayawa cikin masu bikin.
A cewar wani ganau da lamarin ya auku a idonsa ya bayyana wa wakilin mu cewa tirelolin sun kauce ne daga babban titin Nasarawa-Eggon zuwa Lafia babban birnin jihar inda suka tunkari inda ake bikin suka yi sanadin mutuwar mutum biyar nan take wasu da dama kuma suka samu munanan raunuka.
Har Ila yau wani ganau kuma ba jiyau ba ya bayyana cewa dayawa cikin ‘yan bikin sun raunata matuƙa ciki har da wasu fitattun mutane da ba a bayyana sunayensu ba inda a yanzu haka aka garzaya dasu babban asibiti na ƙasa dake birnin tarayya Abuja.
Har da shima shugaban kwamitin shirya babban taron, Barr. Alaku Dennis ya samu rauni kuma a halin yanzu shima yana kwance a asibitin Nasarawa-Eggon yana samun kulawar likitoci.
A nasa ɓangaren wani mai magana da yawun ƙungiyar dake shirya bikin na ƙasa baki ɗaya wato Chief Gale Esson John ya kwatanta haduran a matsayin mai tsananin muni inda ya ƙara da cewa kasancewar ya auku ne a wajen da ake gudanar da babban bikin ƙarshen shekara kamar wannan inda yace tabbas a yanzu abinda ke ɗagawa mutane hankali shine yanayin halin juyayi da iyayen mamatan za su kasance bayan sun samu labarin aukuwar mummunar lamarin.
A halin da ake ciki dai tuni wannan kwamiti da ke shirya bikin ta sanar da dakatar da bikin cikin gaggawa jim kaɗan bayan aukuwar bala’in inda ta jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa tare da addu’ar Allah ya gafarta musu.
Shima a nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar ta Nassarawa Eggon, Barr. Iliya Ibn Aliyu wanda ya ziyarci inda lamarin ya auku cikin gaggawa jim kaɗan bayan ya samu labarin ya taya al”ummar ƙasar Eggon baki ɗaya jimamin rashin da suka yi na ‘yan uwan nasu tare da waɗanda suka raunata.
Shugaban Barr. Aliyu ya kuma bayyana hatsarin a matsayin mafi muni a yankin inda ya kuma yi amfani da damar yayi kira na musamman ga gwamnati ta yi wa Allah ta yi wa Annabi ta nemi mafitar gaggawa wa hanyoyin musamman babban titin don magance aukuwar irin mummunar lamarin nan gaba.
