Katsina: Sanannen dillalin ƙwaya da wasu biyu sun rasu yayin arangamar matasa da jami’an tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mutane uku sun rasu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wata arangama da ta ƙunshi jami’an tsaro da wasu da ake zargin dillalan ƙwaya ne a yankin Kwabron Ɗorawa na Unguwar Nayalle a Rukunin Gidajen Sabuwar Unguwa da ke cikin garin Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne a lokacin da jami’an tsaro suka yi yunƙurin kamawa, ƙwace wayar salula da wasu miyagun ƙwayoyi daga ɗaya daga cikin dillalan a yankin mai suna Uzairu, wanda aka fi sani da ‘Ƙuda’.

Wani shaida ya ce al’amarin ya yi ƙamari ne a lokacin da Ƙudan ya ƙi amincewa da kamen jami’an inda ya garzaya ya gayyato abokanansa domin ƙwato wayarsa da jami’an suka karɓe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa bayan wani daga cikin jami’an ya bindige shi.

A yayin rikicin ne aka ƙone wani ofishin jami’an Hukumar Sibil Defense da wasu babura daga wasu fusatattun matasa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq ya tabbatar da aukuwar lamarin a jiya Lahadi, inda ya ce rikicin ya sake faɗaɗa ne a lokacin da ake jana’izar mamacin bayan wasu alburusai biyu da aka yi kuren harbowa sun samu mutane biyu, waɗanda aka yi gaggawar kai su wani asibiti mafi kusa da inda abin ya faru.

Don haka ne DSP Sadiq ya kirayi al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu a irin waɗannan halayen.

By Babaji