NSCDC a Katsina ta kama mutane takwas da ake zargi da ƙona ofishin su

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar SC Buhari Hamisu ya fitar da sanarwar haka.

Lamarin ya faru ne bayan da ‘yan sanda sun kai samame a unguwar inda suka kama Uzairu da aka sani da (DAN’KUDA) da ake zargi yana ɗillancin miyagun ƙwayoyi.

To sai dai wanda ake zargin yayi ƙoƙarin amfani da ƙarfi wajan kuɓucewa a hannun su ,sai su ka harbe shi har lahira bayan da yayi ƙoƙarin ƙwace bindiga a hannun su.

Ganin haka wasu ɓata gari domin su nuna hushin su suka kaiwa ‘yan sandan hari wanda nan ma mutum biyu suka rasa ransu.

Bayan wannan arangama waɗannan ɓata gari sun ƙona ofishin yan Civil Defence a unguwar,sanan suka wuce unguwar filin Kanada nan ma sunyi kokarin ƙona ofishin Yan Civil Defence da na Yan sanda amma basu sami nasara ba.

Kan haka ne kwamandan rundunar Civil Defence a jihar AD Motoci ya kafa kwamitin mutum bakwai don su gano musabbabin afkuwar lamarin.

Ya kuma yabawa jami’an sa bisa nasarar da suka samu na kama mutane takwas inda ya tabbatar wa al’ummar jihar Katsina cewa hukumar sa za su cigaba da kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.

Kwamandan ya kuma yi kira ga sauran hukumomin tsaro a jihar da su sami haɗin gwiwa don tabbatar da tsaro a jihar.

Ya gargaɗi masu yiwa tattalin arzikin jihar zagon ƙasa da sauran ɓata gari da ko su daina ko kuma su fuskanci doka.

Kwanan baya sai da yan sanda su ka ɗauki kwanaki suna bata kashi da ƙauraye a unguwar wanda nan ma sai da aka rasa rayuka.

By ukarofi