Shugaba mai gaskiya ya fi mai ƙasaita da dokinsa – Queen Amina

Spread the love

Ba wanda zai gina ganuwa idan zuciyarsa ta rushe – Sarauniya Amina ta Zazzau

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, sannunku da jimirin bibiyar mu a wannan jarida ta Blueprint Manhaja.

A makon da ya wuce, shafin Gimbiya ya zaƙulo sarauniya kuma jarumar ƙasar Zazzau, Queen Amina of Zazzau a matsayin gimbiyar mu ta mako, saidai labarin nata bai kai ga ƙarewa ba shafin namu ya kai ƙarshe, don haka ne ma muka yi alƙawarin ci gaba a mako mai zuwa wato wannan satin.

Idan kuna biye da mu, mun soma da bayanin ƙurciyar Sarauniya Amina, inda muka ce tun a yarinta ta nuna alamun jarumta, domin a lokacin da yara ‘yan uwanta ke wurin wasa, tarihi ya tabbatar da Sarauniya Amina tana wurin koyon ɗaukar takobi da kuma hawa doki, wanda tun a nan ta nuna ita ɗin ta daban ce a mata, kuma an haikanto za ta yi abinda da yawa a mata ba su yi ba.

Mun bayyana yadda Queeen Amina ta samu sarautar Zazzau, da yadda ta zama sarauniya ta farko a birnin mai cikakken iko, wanda hakan na nufin ita ce sarauniya ta farko da ta hau mulki ta yadda kowane namijin da ya yi sarauta yake yi, don haka ta samu duk wani iko da dama da sarki ke samu.

Ba kuwa don komai ta samu wannan ba face irin jarumtar da ta nuna, da kuma yadda take da dukan ababen da ake buƙata ga shugaban da zai mulki ƙasar.

Mun kuma taɓo yadda ta mulki ƙasarta cikin hikima da ƙwarewa, sannan kuma mun bayyyana yadda ta ci yaƙi da dama, da kuma irin jarumtar ta ta kasancewa mai jagorantar kusan duk yaƙin da ta yi.

Mun kawo wa masu karatu irin nasarorin da ta samu, waɗanda suke da yawa kuma masu nauyin da tarihi ya san da su kuma ya ba ta damar zama jerin sarakunan da duniya suka san da zamansu kuma Afirka ke kiran sunata da alfahari.

Mun soma kawo irin ƙalubalen da ta fuskatanta a matsayin sarauniya, inda ta haɗu da rashin haɗin kai na wasu daga cikin masu faɗa a ji a masarauntar, a cewar su bai kamata a ba wa mace irin wannan dama da ta samu ba, wato ta zama sarauniya mai cikakken ido. Sannan mun kawo yadda wasu abokanen gaba suka yi amfani da ƙasar tata wurin yunƙurin cin ta da yaƙi, ta hanyar kutsowa cikin al’ummarta don raraba kawunansu a ƙoƙarin ruwa wutar rigima ta cikin gida.

Ba mu samu damar dogon bayani kan ƙalubalen da Queen Amina of Zazzau ta fuskanta ba sakamakon kai wa adadin kalmomin da shafin namu zai iya ɗauka. Don haka za mu soma daga nan.

Idan kun shirya, Aisha Asas ce ɗauke da ci gaban tarihin jarumar ƙasar Hausa, Sarauniya Amina ta Zazzau. A sha karatu lafiya.

Rayuwar Sarauniya Amina ta ɗauki dogon lokaci cikin ƙalubale wanda idan muka tsaya bayyana su za mu ɗauki kalmomi da dama, saidai idan mai karatu zai yi duba da idon basira kan irin rayuwar da ta gina da kuma yadda take fuskantar abokan gaba ba tare da tsoro ba, da kuma irin wuraren da ta ci da yaƙi, zai iya amincewa hakan ba abu ne mai sauƙi ba.

A wasu ruwayoyi, an ce Sarauniya Amina ta rayuwa ba tare da aure ba, sakamakon mayar da hankali kan mulki da yaƙi, wanda hakan ma na ɗaya daga cikin manyan ƙalubale da kuma irin sadaukarwar da ta yi ga ƙasarta.

Idan mun kalli abin da idon basira, za mu fahimci cewa, a matsayinta ta sarauniya mai irin wannan iko da kuma kasancewar ta jaruma mai ƙarfin yaƙi, zaɓar mijin aure zai iya zama babban aiki, wanda idan ta yi kuskure zai shafi makomar ƙasarta baki ɗaya. Kuma kasancewar ba a gane maƙiyi a fuska, ba lallai ba ne duk wanda zai yi muradin auren ta ya zama yana da ra’ayi da fata ga ƙasar ta irin wanda take da shi. Da wannan ne ta zaɓi ƙasarta akan nata farin cikin.

Idan mun yi gaba zuwa ga mutuwa, wadda ta zama rigar kowa, kuma duk tsawon rai da tasirin ka, ita ɗin dai ce ƙarshen da za ka yi.

A ɓangaren rasuwar sarauniya Amina, masana tarihi sun samu saɓani kan yadda mutuwa ta riske ta, ma’ana sila da kuma wurin da ta yi wafati, saidai mafi yawa, kuma masu rinjayen a ruwayoyin sun ce ta haɗu da mutuwa ne a wurin yaƙi, saɓanin waɗanda ke faɗa cewa ta rasu a cikin masarauta.

Ta rasu ne yayin wani yaƙi a yankin Atagara ( yana cikin ƙasar Nupeland), a shekara ta 1610 CE. Saidai za mu iya cewa, gangar cikinta ce kawai ta mutu, domin bayan rasuwarta sunan ta bai fice daga bakuna mutane da kuma ayyukansu ba, inda ta zama allon kwaikwayo ba a mata ba har a maza. Ana ɗaukar sunanta a matsayin hujja da ke nuna ƙarfin da mace take da shi, wanda hakan ya sa ra’ayin wasu da dama ya canza kan irin ababen da mace za ta iya yi.

Tasirin Sarauniya Amina ba zai iya zayyanuwa a cikin kalmomi kaɗan ba, saidai mu ce ta taɓa rayuka da dama a lokacin rayuwarta, inda bayan rasuwarta ko ince har yanzu wasu gidaje a Zazzau na riƙe da wasu kayanta a matsayin tarihi da ke cike da alfahari.

Queen Amina ta yi amon da ba a Najeriya ko Afirka ba, duniya baki ɗaya ta zama allon kwaikwayo ga mata, kuma suna yawan ambatar ta a matsayin alamu ta jarumtar mata, tare da jinjinawa namijin ƙoƙarin da ta yi a zamanin da take raye.

Har zuwa yanzu, wuraren da ta ci yaƙi, ba a daina kiran katangar da take yi da suna Ganuwar Amina ba, hakan na nufin tarihin na alfahari da ita har zuwa yanzu.

Kamar yadda na gani a wani rubutu na wani bature a kwanaki, ya bayyana yadda mutum-mutumi (statue) da aka ƙera na Queen Amina ke bayyana yadda tarihi ke son tunawa da ita, inda ya ce hanya ce ta tunawa da ita kan jarumta da tasirin ta a matsayin sarauniya mace.

Amina ta zama garkuwa da ke nuna jarumtar mata, ba wa mata ƙarfin ƙwiwar amincewa komai ma za su iya, sannan ta ilimantar da su sanin darajar su, ta hanyar lurar da su cewa, duk jarumtar mace tana buƙatar mutunta kanta tare da tsoron Allah kafin ta zama cikakkar mace. Ta kuma bayyana yadda mata suke jarumai masu hangen nesa fiye da yadda duniya ke kallon su.

Sarauniya Amina ta Zazzau ta bar tarihi mai zurfi wanda ke ratsa ƙarni da ƙarni. Ta nuna cewa mulki da jagoranci ba shi buƙatar jinsi, ba kuma na wani ɓangare ne ba, na wanda ya san yaƙi, hikima ne da kuma adalci. Wanda idan mutum ya haɗa waɗannan idon mutane kan kauce daga kallon jinsin sa zuwa kallon namijin ƙoƙarin da yake yi.

Wannan kuwa na tasiri har a matan wannan ƙarni, domin idan mace ta tsaya ta yi ilimi, ta tsunduma harkar kasuwanci ko siyasa, takan jin ita ma za ta iya, kuma duniya za ta ga ta bi sawun saraniya Amina, sarauniyar da ta tabbatar da cewa ƙarfin zuciya da hangen nesa sun fi ƙarfin jiki ko na jinsi tasiri. Sarauniya Amina ta Zazzau, sarauniya mai doki da takobi, amma zuciya cike da hikima.

Shin menene darasin da yake cikin rayuwar Queen Amina of Zazzau?

Tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau ba kawai labari ne na wata jarumar mace da ta yi mulki ba, wadda ta nuna mata sun iya ko za su iya ba, darasi ne mai zurfi ga kowacce mace da ke son ta san ƙimarta, ta yarda da kanta, ta kuma yi rayuwa mai ma’ana. 

Akwai abubuwa da dama da mata na yau za su iya koya daga rayuwarta, wadda za mu ɗan kawo wasu daga ciki;

ƙarfin zuciya da jajircewa: Amina ta tashi a ƙarnin da mata ba su samu walwala sosai ba ta fuskar ‘yanci, duk da haka ta nuna wa mata darasin cewa, mace fa ba ta buƙatar jira har sai an sanar da ita ta iso ko ta kai lokacin da za ta iya yin wani abu, maimakon haka ita da kanta ne za ta nuna a aikace cewa ta cancance shi. Kenan zaman da mata ke yi suna jiran a ce masu ga shi, ko tashi mu kama miki, duk wata hanya ce ta lalaci. Idan har kina son a san za ki iya, sai kin nuna hakan a aikace.

A matsayinki ta mace, za ki iya cewa, “idan har Amina za ta iya mulkar ƙasa a ƙarni na 16 mai cike da ƙalubale na yaƙi da matsaloli, ni ma zan iya fitar da kaina daga duhu zuwa haske.”

Ilimi da basira su ne makamin mace:

Duk da cewa Sarauniya Amina ta shahara da yaƙi, amma makamin da ta fi dogaro da shi ba takobi ba ne, ilimi ne da amfani da basirar da take da ita.

Ta fahimci cewa, kafin ta yi nasara tana buƙatar ilimi don sanin yadda za ta tsara sojojinta, da yadda za ta shirya kasunwanci, da kuma uwa uba sanin yadda za ta yi hulɗe da ƙasashe da fahimtar tsarin ƙasashen da ta ƙulla alaƙa da su. Duk wannan ba ya buƙatar takobi.

Darasin da mata za su iya koya anan shi ne; karatun mace fitila ce da za ta iya haska mata hanyar da burinta yake, kuma ilimin nan ba nata kaɗai ba ne, makami ne da zai kare ta daga rauni, amma kuma hanya ce da ke haskaka al’umma baki ɗaya; domin kamar yadda aka faɗa ‘wanda ya ilimantar da mace ɗaya kamar ya ilimantar da al’umma ne baki ɗaya’.

Gudunmuwar mata a cigaban al’umma:

Sarauniya Amina ta nuna cewa, mata na da muhimmiyar rawa da za su iya takawa a gina al’umma, anan muna maganar baya ga sananiyar hanyar da suke ba wa al’umma gudunmuwa, wato renon ‘ya’ya da ba su tarbiyya.

Amina ta gina hanyoyin kasuwanci, ta wanzar da tsaro, wanda hakan na nufin ita ma mace za ta iya bayar da gudunmuwa a ɓangarori da dama na cigaban al’ummarta.

Tsoron Allah da adalci a jagoranci:

Sarauniya Amina ta nuna cewa, shugabanci ba yana nufin nuna iko da ƙarfi ba ne, yana nufin nuna adalci ne.

A cikin wasu daga cikin maganganunta da aka taskace, Queen Amina ta ce, “Shugaba mai gaskiya ya fi mai ƙasaita da dokinsa.”

Ma’ana shugaba mai adalci ya fi tasiri fiye da mai ƙarfin sojoji da dawakai. Wannan zai iya zama izna ga matan da ke shugabantar wasu wurare; ko a gida, makaranta, kasuwanci ko kuma gwamnati, su san cewa adalci da tsoron Allah su ne ginshiƙi kuma ƙashin bayan duk wata nasara da za su samu. Wannan kuwa ya zama babban ci gaba da ake samu a tsakanin mata na wannan lokaci, saboda matan ma sun zama kan gaba wurin nuna isa a duk lokacin da Allah ya ɗora su kan wani matsayi.

Abinda aka fi sanin mace da shi shi ne tausayi, don haka a duk lokacin da aka ɗora ta kan wani muƙami ana sa ran ganin adalci da tsoron Allah a cikin ayyukanta, saidai a lokuta da dama suna amfani da matsayin nasu wurin taka wanda suka ga dama, tare da yunƙurin cika burinsu ba tare da la’akari da waɗanda za su iya tauyewa a ƙoƙarinyin hakan ba.

Zaman lafiya da haɗin kai:

Duk da kasancewar Sarauniya Amina jaruma mai ƙarfin soji, ta nuna muhimmancin zaman lafiya da yadda ta zaɓe shi fiye da yaƙi, inda tarihi ya bayyana ta kafa yarjejeniya ba adadi tsakanin ƙasashen da ke da husuma ko gadon hamayya a tsakaninsu.

Kamar yadda aka faɗa ‘zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki’, ƙueen Amina ta tabbatar da mace na iya zama jakadiyar zaman lafiya a matsayinta ta uwa ko shugaba ga al’umma matuƙar ta yi amfani da hikima da kuma tausayi wanda ya kasance a cikin halittarta.

Rayuwar Sarauniya Amina ta Zazzau ta kasance tamkar fitila ga mata. A duk rayuwar da mace zata fuskanta, duk nauyin ƙalubalen da ke cikinta, rayuwar sarauniyar za ta iya sanar da ita cewa, akwai haske a ƙarshen kowane kogo, kuma za ta iya kai wa ga ci, duk kuwa da tarisin waɗanda ke cewa ba zai yiwu ba.

Da wannan za mu iya cewa, ko a yau mace ta tsayu akan gaskiya da ilimi, to tabbas Zazzau na cikin zuciyarta.

By ukarofi