
Dags BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kwara Abdulrahman AbdulRazaq ya sanar da sako baki ɗaya mutane 38 da aka yi garkuwa da su a Cocin Christ Apostlic (CAC) na Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti cikin aminci.
A yau Lahadi mutanen suka shaƙi iskar ƴanci bayan atisayen da ya ƙunshi ɓangarorin hukumomin tsaro na manyan matakan gwamnati.
A sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar, Gwamna AbdulRazaq ya danganta nasarar ceto mutanen da shiga tsakani na Shugaba Bola Tinubu.
A cewar gwamnan, Tinubu bai tsaya a sanya ido wajen ceton ba, hat ma da sadaukar da bulaguronsa na aiki a taron G20 na Afirka ta Kudu domin ganin yadda za ta kasance a halin lamuran tsaro a jihohin Kwara da Kebbi.
Ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya umarci a tsaurara tsaro a ƙauyukan da al’amarin ya shafa, lamarin da ya haɗa jami’an hukumomin tsaro da dama waje guda.
Kazalika, ya yaba wa hukumomin tsaro a matakin jiha da ma ƙasa baki ɗaya bisa hoɓɓasa da suka yi ciki har da ofishin mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA), DSS, sojoji, NIA da rundunar ƴan sanda.
A ƙarshe, ya jinjina wa gudumawar jagororin al’umma, cibiyoyin addini da ɗaukacin al’umma, waɗanda addu’o’insu suka taimaka wajen ceto mutanen.
