
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Uba Sani, ta yi watsi da zarge-zargen da tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufa’i ya yi akanta cewa ta biya ƴan bindiga Naira biliyan 1.
Ta bayyana kalaman, waɗanda aka yi su yayin hira da gidan talabijin na Channels a matsayin ƙarya da ake nufin siyasantarwa, kuma abin da babu hujja a kai.
A wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida, Dakta Sule Shu’aibu (SAN) ya fitar, gwamnatin ta ce zarge-zargen El-Rufa’i babu ƙamshin gaskiya acikinsu, tana mai zargin sa da yunƙurin ruɗar da al’umma da kushe nasarorin da aka samu wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Sanarwar ta kuma soki tsohon gwamnan kan yadda yake ƙoƙarin yin amfani da al’amarin tsaro don cimma wata manufar siyasa, inda ta ce bai dace a samu tsohon gwamna da aikata irin hakan ba.
Gwamnatin ta bayyana cewa Gwamna Uba Sani bai taɓa amincewa, tattaunawa ko biyan wani kuɗi ga wata ƙungiyar ƴan ta’adda ba.
Kazalika, kwamishinan ya ce gwamnan ya sha nanata haka a tattaunawa da ƴan jarida da zama ko taruka da masu ruwa da tsaki, inda ya ƙara da cewa: “ko Naira ɗaya, kai ko da kwabo ɗaya.”
Har’ilayau, sanarwar ta ce a baya ofishin mai ba Shugaban ƙasa shawara akan harkar tsaro (ONSA) ta yi waste da irin ikirarin na El-Rufa’i wanda ba shi asali kuma abinda bai dace da tsarin gudanar da lamuran tsaro a ƙasar ba.
