Ilimi shi ne ke ba mace damar tsayawa da ƙafarta ko an juya mata baya – Sarauniya Cleopatra

Spread the love

Idan mace ta san darajar kanta, duniya za ta san darajar ta – Sarauniya Cleopatra

Daga AISHA ASAS

Idan kuna neman macen da za a iya cewa ta haɗa komai da mata ke burin samu na daga kyau, farin jini da kuma mulki.

Macen da za mu iya cewa mai kamar maza, wani sa’in ma har ta fi wasu mazan. Cleopatra ta kasance sarauniyar da ta kafa tarihin da har yau ba a samu wadda ta maye gurbinta ba, saidai a samu masu kusa da ita. 

A ɓangare guda, za mu iya cewa, ta aikata ababe na ƙarfin hali da duniya ke ganin su a matsayin abun ƙyama da har yau ake mamakin su duk da sunan samun mulki. 

Kamar yadda mutane ke faɗa cewa, wai ba a cika haɗe wa mace ababe guda uku wuri ɗaya ba, wato kyau, ilimi da kuma zurfin tunani ba, saidai akan Cleopatra wannan magana ta samu musantawa, domin ta kasance mace mai kyau da farin jini da suka sa manyan jarumai ke ribibinta, sannan tana da ilimi mai yawa, domin tarihi ya tabbatar da tana jin yaruka har guda tara. Baya ga haka sarauniya Cleopatra ta kasance mace mai hikima da zurfin tunani, wanda ya sa ta yi amfani da kyau da take da shi wurin sace zukatan fitattun jaruman lokacin kuma ta sanya hikima wurin kissa da har ta mallake ƙwaƙwalwarsu, inda tarihi ya bayyana cewa, har yaƙi suke yi saboda ita, wato dai amfani da makaminsu wurin cimma muradun ta.

Na san mai karatu zai iya cewa labarin Cleopatra ba shi da alaƙa ko wani abin amfani ga masu karatun wannan shafin na Gimbiya, saidai zan iya cewa, a’a, domin a cikin rayuwarta akwai ababe da dama da zai iya zama allon kwaikwayo ga masu karatu, kuma su sami ababen da idan sun masa muhalli a al’adu da rayuwarsu za su iya samun darasin da za su koya da zai iya hana su ko ba su ƙwarin gwiwa ga wani abu da suke yi ko suke shirin yi.

Bari mu soma da jin ko wacce ce sarauniya Cleopatra?

Cleopatra ɓII Philopator, wadda aka fi sani da Cleopatra ta Masar, an haife ta a shekara ta 69 kafin haihuwar Annabi Isa (K.H.A)  a birnin Aleɗandria, wadda a lokacin ta kasance cibiyar ilimi da fasaha ta duniya.

Cleopatra ta fito daga gidan sarauta na Ptolemaic Dynasty, sarautar da ta samo asali daga ƙasar Girka, duk da cewa bayan mutuwar Aleɗander The Great, sarautar ta mamaye Masar.

Tun tana ƙarama, Cleopatra ke nuna alamun kasancewa ta daban a cikin mata, kamar yadda masu azancin magana kan ce, kyakywar safiya tun daga marecen ta ake ganewa. 

An haikanto rayuwarta za ta zama mai cike da manyan al’amari ta sanadiyar irin barisar da take nuna wa tun a ƙananan shekaru da kuma yadda take gudanar da sha’aninta cikin nutsuwa, wanda ya fi ƙarfin shekarunta. 

Ta koyi harsuna da dama, inda tarihi ya ce, ta koyi harsunan Girka, Ibrananci, Latin, da na Masaranci, wadda hakan bai kasance abu sananne a tsakanin matan masarauta ba.

Wannan damar ta harsuna ta ba ta damar tattaunawa da jama’a da dama, da sanin ababubuwan da suka nisanta da ita tunda ba ta buƙatar tafinta don yin magana da masu waɗannan yaren.

Wani abu da ya ƙara zama silar mayar da ita jarumar mace akwai buɗe ido da ta ti a gidan faɗa, wanda yake cike da siyasa. Wannan kuwa na nufin amfani da hikima da dabaru.

Mahaifinta Ptolemy  ɗII, ya sha arangama da rigingimu da ƙasasashen waje. Wannan ya sa Cleopatra ta koyi dabarun siyasa da faɗa tun kafin ta kai shekaru 19.

Bayan mutuwar mahaifinta, Cleopatra ta hau mulki ta hanyar da za mu iya kira da bauɗaɗiya ko ƙazamar hanya, wato ta auren ɗan uwanta na jini Ptolemy ɗIII, wanda a lokacin yake da shekaru 10, ita kuma tana da 18. Hakan ya faru ne dalilin dokar da ke masarautar a lokacin na mace ba ta mulki ita kaɗai sai tare da namiji.

Duk da wannan dokar bai hana mulkin ta amo a tsakanin ƙasashen duniya ba, ta kasance mai ƙarfin magana da kowa zai ji ta, mace mai tsayin daka wurin gyara abinda take ganin bai mata ba. Mai neman shawara daga masana don ganin ta kai inda take muradin kaiwa.

Tarihin ƙalubalen rayuwa ya zafafa ga Cleopatra ne a lokacin da rikicin cikin gida ya kunno kai tsakaninta da ɗan uwanta, wanda ya yi zafi sosai har ya tsorata dattawan Masar. Zafin lamarin ne ya sa suka zaɓi fitar da ita daga fadar. 

A lokacin ne ta yi ƙaura zuwa Syria wanda wasu ke ganin hakan a matsayin tsoro, ta gudu don tsira da ranta. Saidai a wurin Cleopatra tafiyar wata dama ce ta yin shiri domin dawowa da ƙarfinta.

Anan ne ta yi amfani da ilimin ta da kyau tare da hikima wurin tara dakaru da masoyan da za su iya bada ransu domin farin cikinta. Daga nan ne ta fara shirin yadda za ta dawo kan karagar mulki ta hanyar amfani da diflomasiyya da ƙarfin soja.

A lokacin da rikicin ke tsananta a Masar, babban jagoran Roma mai ƙarfin iko da ji da jarumta, Julius Caesar, ya isa Aleɗandria domin sasanta rikicin. Anan ne Cleopatra ta yi amfani da baiwa biyu da take da ita wurin janyo hankalin Caesar, wato kyau da hikima.

Tarihi ya bayyana cewa, ta naɗe kanta a kafet ne na alfarma, aka ɗauko ta aka shiga da ita faɗar Caesar, har aka shiga da ita ɗakin sarkin ba wanda ya sani, sai a wurin shimfiɗa kafet ɗin ne aka tarar da ita.

Baya ga kyakyawar surarta da ta bayyana wadda ke ɗaukar hankalin mazaje, Caesar ya yaba matuƙa da irin hikimar da ta yi amfani da ita wurin kawo kanta wanda idan ta zo kai tsaye hakan zai iya yi mata wuyar gani ba tare da bin doka ba.

A wani ɓangare kuwa ya fahimci cewa Cleopatra ba sarauniya ce kawai ba, mace ce mai jarumta, domin irin matsayi da yake da shi, da ƙarfin iko da tsoron sa da ake yi, zai iya sa tsoron tunkarar sa ba tare da amincewar sa ba.

Cleopatra ta yi amfani da makamin kyau da hikima ta sace zuciyar jarumi babban jagoran Roma, inda ido rufe ya goyi bayanta suka lashe rikicin na cikin gida. Ta dawo kan karagar mulki cikin ƙarin ƙima da ɗaukaka. Kuma a nan ne tarihi ya sauya, domin ta dawo kan mulki ne a matsayin sarauniyar Masar mai cikakken iko, mai cin gashin kanta ba tare da laɓawa da aure ba kamar yadda ake yi a baya, duk da cewa kasancewar ta tare da Caesar ya ƙara wa masarautar tagomashi, ga uwa uba taya ta mulkin da yake yi a matsayin sa na abokin rayuwarta. 

Cikin zurfi na tunanin sarauniya Cleopatra akwai faɗaɗa hikimarta, domin ba ta tsaya a iya baiwar kyau da take da shi wanda take sa jaruman maza russuna mata ba, ko amfani da dabarun siyasa ba, ta zamo mai fasaha wurin mulki.

Ta gyara tsarin haraji, ta buɗe kasuwanni, ta tallafa wa manoma, kuma ta dawo da Aleɗandria a matsayin cibiyar karatu da bincike.

Cleopatra ta bayar da gudunmuwa sosai ga mata, domin tana ƙarfafa ilimi ga mata. Ana cewa ta kan ce: “Ilimi shi ne ke ba mace damar tsayawa da kanta, ko da duniya ta juya mata baya.”

A cikin tarihi da labaran da aka ruwaito daga Cleopatra, ta kan ba mata shawarar su kasance masu ilimi, mutunta kai da ƙima, kuma kar su tsaya a iya kyan fuskarsu. A cikin ɗaya daga cikin maganganunta kan wannan ɓangaren akwai inda ta ke cewa: “Idan mace ta san darajar kanta, duniya za ta san darajar ta.”

Ta kuma taɓa faɗar cewa: “Kyawon mace bai tsaya a iya fuskarta ba, yana cikin abinda take tunani, da yadda take tafiyar da rayuwarta.”

A ɓangaren kwalliya kuwa za mu iya cewa sarauniya Cleopatra ta kasance allon kwaikwayo ga matan lokacin ta. Ta shahara wurin kula da kanta. Ita ce ta kafa ɗaya daga cikin sirrikan kwalliya ta mata da har yanzu duniya ke tafiya da su. Ta yi amfani da man zaitun, madara, zuma da kuma wasu itattuwa wurin kula da fatarta da kuma gashi.

Sarauniya Cleopatra ta amince da kyakwawar mace na da tasiri a siyasa da kuma hulɗa da jama’a, saidai ta jaddada cewa: Kwalliya ta gaskiya tana fitowa daga cikin mace na daga yadda take tafiyar da hankalinta da nutsuwarta.

A yau masana kwalliya suna ganin Cleopatra a matsayin gimbiya ta farko a duniya da ta sada kwalliya ga ilimi tare da fasaha.

Cleopatra ta rasu a shekara ta 30 kafin haihuwar Annabi Isa (K.H.A), bayan sojojin Roma sun mamaye Masar. Tarihi ya ruwaito cewa, ta mutu da kanta ne, wato ta kashe kanta, domin gujewa kamata, wanda hakan zai sa ta kasance cikin ganimar yaƙi.

Rayuwar sarauniya Cleopatra ya sanar da duniya cewa, mace ma za ta iya mulki kuma ta bayar da irin abinda ake fatar samu.

Wani marubuci mai suna Plutarch ya rubuta cewa: “Cleopatra ta kasance mace mai hikima fiye da kowa a zamaninta. Kalar murya da nutsuwar maganarta suna da ƙarfin da ke iya juyar da zuciyar mutum.”

A yau ana ganin Cleopatra a matsayin alamar ikon mace a siyasa, kasuwanci da fasaha. A fina-finai, littattafai da kayan ado ana ci gaba da amfani da sunanta a matsayin girmamawa ga mace mai ƙarfi ko kyau.

A Afirka musamman ƙasar Masar ana koyar da tarihin Cleopatra a makarantu a matsayin misali na macen da ta yi mulki cikin hikima da ƙwarewa.

A cikin kalamanta na ƙarshe, Cleopatra ta ce, “Zuciyar mace ita ce tauraron da ke haskaka duniya, amma sai ta bari ya yi haske da gaske.”

By ukarofi