2027: Zamanin ɗauki ɗora na ‘yan takara ya ƙare a Zamfara – Shinkafi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD. Gusau

Jigo a jam’iyyar All Progressive Congress APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya sake jaddada cewa zamanin da ake ɗauki ɗorar ‘yan takara a ƙarƙashin jam’iyyar a jihar ya ƙare, musamma a zaɓen shekarar 2027.

Ya yi wannan sanarwar a wani taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyar Wamban Shinkafi Democratic Front ta shirya a Gusau yau Talata.

“Lokacin da ake ɗauki ɗorar ‘yan takara a ƙarƙashin babbar jam’iyyarmu ta APC ya kawo ƙarshe musamman a babban zaɓen 2027 mai zuwa. Ba zamu sake amince wa da shi ba kuma dole ne a bai wa kowa daga cikin membobin jam’iyyarmu damar yin takara daidai gwargwado don samun zaman lafiya da ci gaban jam’iyyarmu.” Shinkafi ya ce

A cewarsa, APC a Zamfara tsintsiya ce maɗaurin ki ɗaya, yana mai jaddada cewa dole ne a ba kowa dama don yin takara a kowane muƙami na siyasa ƙarƙashin jam’iyyar APC a shekarar 2027 a jihar.

Shinkafi ya ƙara da cewa zai yi takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar APC a zaɓen 2027 mai zuwa a jihar Zamfara.

“Zan tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin babbar jam’iyyarmu ta APC a shekarar 2027 a Zamfara domin ceto Zamfara daga rashin tsaron da ke addabar jihar”. Shinkafi ya ƙara da cewa

Shinkafi ya ƙara da cewa, Ƙungiyar sa ta Wamban Shinkafi Democratic Front ta amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a shekarar 2029 a ƙarƙashin APC.

Ya ce ƙungiyar sa ta Democratic Front za ta ci gaba da kasancewa ‘yan ƙasa masu bin doka da oda kuma masu biyayya ga shugabancin APC daga matakin ƙasa zuwa jiha domin nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayanta a jihar Zamfara da su ci gaba da haɗa kai don nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen gama gari da za a yi a ƙasar nan a 2027.

By ukarofi