Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tun bayan maganganun Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, wanda ya laƙanci Nijeriya a matsayin “ƙasa mai matsalar cin zarafin addini” tare da yin barazanar aikewa da sojojin Amurka ƙasar, cece-kuce ya kunno kai a kafafen yaɗa labarai da kuma dandalin sada zumunta. Sai dai kafin wannan rikici ya yi zafi, wani fitaccen sanata na Amurka, Ted Cruz, shine ya daɗe yana rura wutar wannan tuhuma ta ‘kisan Kiristoci’ a Nijeriya tuni, yana mai cewa, gwamnati na nuna son rai da wariyar addini. Wannan rahoto ya kawo tarihin mutumin da ya fara iza wutar zargi daga nisan duniya fiye da kilomita dubu shida.
Tarihi da asalinsa:
An haifi Cruz da sunan Rafael Edward Cruz a Calgary, Canada a 1970. Mahaifinsa, Rafael Bienvenido Cruz, ɗan Cuba ne kuma malamin addini mai ra’ayin kishin addini sosai, wanda ya gina ɗansa cikin tsattsauran ra’ayin addini da kishin aƙidar siyasa.
Ya samu asalin zama ɗan Amurka daga mahaifiyarsa Eleanor Elizabeth ’yar jihar Delaware.
Cruz ya yi karatu a jami’ar Princeton a fannin manufofin jama’a, sannan ya samu digirin lauya a Harvard Law School. Bayan haka ya yi aikin baiwa babban Alƙalin Kotun ƙoli, William Rehnƙuist shawara — babban gata ne ga matashin lauya.
Daga baya ya yi aiki a lauyoyi masu zaman kansu, sannan ya shiga gwamnatin Shugaba George Bush a matsayin mai ba da shawara kan manufofin cikin gida. Ya riƙe muƙamin babban lauya (Solicitor-General) na jihar Teɗas daga 2003 zuwa 2008, inda ya kare muƙamai a gaban Kotun ƙoli na Amurka har sau tara — abin da ya ƙara masa suna.
Haskawarsa a siyasa:
Cruz ya fara yin suna sosai a 2012 bayan goyon bayan Tea Party — wani ɓangaren jam’iyyar Republican mai zafi.
A 2013 ya kasance kan gaba wajen tayar da zaune tsaye da ta kai ga rufe gwamnatin tarayya saboda kira da ya yi a rusa dokar Obamacare. A lokacin ya karanta littafin yara Green Eggs and Ham a gaban majalisa na tsawon sa’o’i 21, abin da ya fusata wasu shugabannin jam’iyyarsa amma ya ba shi ƙarin farin jini a wajen masu ra’ayin tsattsauran kishin jam’iyya.
Wannan hali nasa na yin abinda ya ga dama ko da kuwa ya sabawa shugabanni ya yi tasiri matuƙa wajen gina surarsa — sanata mai sa ƙura kuma mai tayar da cece-kuce.
Ga magoya bayansa, shi ne “mai kare kundin tsarin mulki da imaninsa”. Ga abokan adawarsa, kuma mai tsokana da nuna isa ne.
ƙoƙarin zama shugaban ƙasa:
A 2016 ya tsaya takarar shugaban ƙasa, yana da goyon bayan mabiya aƙidar Evangelical da Tea Party. Ya ci wasu jihohi kamar Iowa da Wisconsin.
Sai dai takarar ta rikiɗe zuwa rikici tsakaninsa da Donald Trump, wanda har ya kai ga Trump na zagin matar Cruz da mahaifinsa. Cruz ma ya ce Trump “mai karya ne kuma mai zalunci”.
Duk da haka, bayan ya faɗi, sai ya koma goyon bayan Trump — alamar yadda siyasar Amurka ta cika dabaru da sauyin salo.
Aƙidunsa:
Cruz yana tsayawa kan ginshiƙai uku: ra’ayi mai tsauri kan kundin tsarin mulki, aƙidar Kiristanci mai ƙarfi da magana da jama’a a matsayin yana yi musu faɗa.
Ya yi adawa da: zubar da ciki, aurar jinsi ɗaya, ƙuntata yaɗuwar bindiga da ƙarin kashe kuɗaɗen gwamnati.
A wajen manufofin ƙasashen waje, babban mabiya Isra’ila ne.
Ted Cruz da Nijeriya:
Shi ne kan gaba wajen zargin cewa ana wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya. A wannan shekarar, ya rubuta takardun neman a sanya Nijeriya a jerin “Country of Particular Concern (CPC)” — wato ƙasashen da ake tuhumar su da keta ‘yancin addini.
Ya yi zargin cewa wasu hukumomin gwamnati a Nijeriya suna amfani da dokokin Shari’a wajen hukunta “ɓatanci” da take ‘yancin addini.
A Satumba ya gabatar da ƙudiri mai neman a sanya takunkumi ga jami’an Nijeriya bisa wannan hujja.
Mene ne CPC?
CPC ita ce matakin hukunci mafi ƙarfi da Amurka ke amfani da shi wajen matsa lamba kan ƙasa.
Hakan ka iya jawo: cire tallafin Amurka, takunkumin diflomasiyya, toshe kuɗaɗe da hulɗa.
Cruz ya ce wajibi ne a hukunta Nijeriya saboda “cin zarafin Kiristoci”.
Akƙdar Evangelical tasa, kishin Isra’ila, da kallon matsalolin Nijeriya ta hanyar addini kawai su ne tushen ra’ayinsa.
Duk da hujjojin shugabannin Kiristoci a Nijeriya masu cewa rikicin Nijeriya ya wuce batun addini — Cruz na ci gaba da ɗora laifi kan ɓangaren gwamnati.
A yayin da gwamnatin Nijeriya ke kare kanta, Cruz na ɗaya daga cikin manyan muryoyin da ke hura wuta a Amurka game da Nijeriya.
Ted Cruz mutum ne da ya kware wajen amfani da harshe, imani, da siyasa wajen motsa jama’a. Duk da cewa ya sha suka kan yadda yake fahimtar rikice-rikicen Nijeriya ta hanyar addini, ba zai daina yin magana ba — domin haka ne siyasar cikin gidansa ta Amurka ta yi masa reno.
A Nijeriya, kalamansa sun tayar da ƙura — amma har yanzu tambaya na nan: ya san ƙasar da ya ke zargi sosai kuwa, ko dai siyasa ce kawai?
