“Iyaye ku daina rufe wa ‘ya’yanku mata ƙofa bayan sun yi aure”
Daga AISHA ASAS
(Ci gaba daga makon jiya)
MANHAJA: Bari mu fara da zancen mutuwar aure da ki ka yi. Za ki samu mata musamman ma a ƙasar Hausa suna shanye duk wani baƙin ciki da cin kashi da suke samu a gidan miji, wanda ba don komai suke yin hakan ba, sai don tsoron rayuwar zawarci, hakan kuwa kan iya kai su ga wata ɓarnar ta saɓa wa Allah. Me za ki ce game da wannan lamarin?
MARIYA DURUMIN IYA: Wannan lamarin na mutuwar aure ba abinda zan faɗa sai dai na ce, innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Na farko dai rayuwar ma gabaɗaya ƙaddara ce, kuma ubangiji Ya riga ya rubuta abinda zai faru ga bawa. Kuma Bahaushe na cewa, ita rayuwa kamar karanta littafi ce, idan ka gama da wannan shafi ka tafi na gaba. Don haka duk abinda Allah Ya rubuta zai sami bawa, ba makawa sai ya same shi. Wannan ya kamata mu fara sawa farko, wato mutuwar aure ƙaddara ce.
Shi ya sa wani lokacin za ki ga an rasa abinda ya kashe wani aure, saboda abin bai taka kara ya karya ba, amma saboda Allah Ya ƙaddara za a rabun, sai kiga ya kasance. A kullum Ina faɗa, iyaye su daina rufewa ‘ya’yansu mata ƙofa, wato kada ka ce da ka yi wa ‘yarka aure ka gama da ita. Ita mace tana rayuwa ne a ƙarƙashin kulawa har ƙarshen rayuwarta. Idan tana gidansu tana ƙarƙashin iyayenta, idan ta yi aure a ƙarkashin mijinta, idan kuwa aka ce yau ba ta da miji, kulawar ta koma ƙarƙashin ɗanta, ko mutanen da ta ke rayuwa tare da su, idan ba ta da ɗa.
To a lokacin da aka ce mace aurenta ya mutu, sai ya kasance ta rasa wannan gatan za ta samu kanta a wata rayuwar da ba a nufe ta da yin irinta ba. Wata za ki ga iyayen ma za su nuna kar ma ta zo gidansu ta ce za ta zauna, don haka sai ki ga wasu sun kama haya, ko in mai abin kanta ce tana da gida sai ta zauna, kinga ta koma ƙarƙashin kanta. Kuma a lokuta da dama za ki ga idan an samu rabuwa matan ake bari da ɗawainiyar yaran. Waɗannan ababe da yawa suke janyo matsaloli. Mace za ta ga idan auren ya mutu ba mai kula da ita, ba mai ɗaukar ɗawainiyar ta, sannan ga yara, ba mai masu hidima, tarbiyyar su za ta lalace, sannan tana tunanin yadda ma mutane za su dinga kallon ta. Wata ba matsalar ɗaukar ɗawainiyar ce take kallo ba, domin za ta iya ɗaukar ɗawainiyar kanta da ta ‘ya’yanta, domin wata ma a gidan mijin nata ma ita ke yin buƙatunta da yaranta, amma kallon da za a yi mata a tsakanin al’ummarta na ta ƙi zaman aure, ko yawon banza ta ke yi. Shi ya sa wata sai ta ga gwara ta haƙura ta zauna ɗin. Ba wai don tana jin daɗin zaman ba, ko ana sauki haƙoƙƙin da Allah Ya ce a bata ba, kawai don ba ta da zaɓi, ba wanda zai yi tunanin wacce irin rayuwa ta yi a gidan mijin, kawai dai ta ƙi zaman aure. Babu mace mai hankali da tana zaune da mijinta lafiya, wataƙila ma har sun haihu ta yi sha’awar su rabu. To yawanci dai irin wannan ke sa matan su haƙura su zauna ba don sun so ba, kuma idan aka yi hakan sai ki ga ɓarna ta biyo baya. Wata idan aka samu mijin ba ya sauke haƙƙinta ko ɗawainiyar ta, idan ta samu wani a waje sai su ƙulla alaƙa, tana samun buƙatunta, kuma tana ƙarƙashin inuwar aure, saboda kawai gujewa irin wannan. Kinga kuwa hakan ne babbar ɓarnar.
Dole ne al’umma ta ba wa zawarawa dama su yi rayuwa kamar kowacce mace, domin wadda ta ke zaune gidan miji ba dubarar ta ce ta zaunar da ita ba, ita ma wadda aurenta ya mutu, ƙaddarar ta ce ta zo a haka.
kin taɓo zancen shashancin da matasa da ke jami’o’i ke shimfiɗawa a rayuwar karatunsu, duk da cewa ba a taru aka zama ɗaya ba, amma duk da hakan akan samu wasu suna yi wa ɗaliban jami’a kuɗin gora, dalilin kenan da har yau ake samun iyaye ko mazajen da ke ƙin barin ‘ya’yansu ko matansu karatun gaba da sakandare. Ko akwai wani abu da wannan gidauniyar taku ke yi na wayar da kai, da bambance wa al’umma tsakanin tsakuwa da aya kan lamarin karatun zamani ga matasa mata?
To dama duk inda aka samu mutane sun haɗu, za ki samu akwai na kirki akwai kuma ɓata gari, musamman ma irin haɗuwar da ake yi a makarantun gaba da sakandare, kusan kowa ma matashi ne, ana ganiyar samartaka ko ‘yanmatanci. Kuma ga dama da suke ganin sun samu, na ba mai matsa maka ka shiga aji, ba mai sa ka saka kayan makaranta. To wani sai ya ga ya samu ‘yanci ba kamar ƙaramar makaranta da babba ba, domin haka sai ya ga sakewa ta zo mashi, tunda a baya yana a takure ne, yanzu ko zai iya fita lokacin da ya ga dama, ya dawo lokacin da yake so duk da sunan karatu ba tare da iyayen sun fahimci komai ba. To wannan ‘yanci da matasa ke samu, wani lokacin sai ya ɗan canza masu tunani, maimakon a tsaya a yi abinda ya kamata, sai kuma a haɗu da gurɓatattun abokane, sai wasu abubuwa su shigo. To amma wannan abu ba yana faruwa a iya makarantun gaba da sakandare ba ne, yana faruwa a ko’ina ma, domin yanzu a yaran da ke unguwa ma, waɗanda ba su je makaranta ba ma ana samun masu shaye-shaye, su dami mutane da sace-sace, da rikicin daba. Su ma matan gasu nan, yau ta shiga nan gidan, gobe a gan ta can gidan biki, yawo ta ko’ina ganin ta ake yi, sai ki samu a irin haka ta haɗa kanta da shaye-shaye, ko haɗuwa da samari waɗanda ba na kirki ba.
Don haka iyaye su fahimci cewa ita lalacewar tarbiyya ba a iya makaranta ta tsaya ba, don haka nake ba su shawara, kada ya zama dalilin da zai hana su barin ‘ya’yansu su yi karatu ba. Abinda kawai ya kamace su tun farko ya zama sun ba wa ‘ya’yansu ingantacciyar tarbiyya, kuma idan sun tura su makarantun gaba da sakandare ya kasance suna ba su kulawar da ya kamata.
Idan mahaifi ya san ba shi da abin ɗaukar ɗawainiyar karatun ‘yarsa, to kada ya tura ta. Domin idan ta je makarantar, ya kasance ita ke ɗaukar ɗawainiyar karatunta, to nan ma an gudu ne ba a tsira ba, dole abinda ba a so ɗin zai iya faruwa. Don haka ni abinda zan ba wa iyaye shawara kuma ni na yarda da shi, ba abinda ya fi a rayuwar mace kamar ɗora ta kan hanyar neman ilimi, har zuwa lokacin da ta samu miji, idan kuma mijin da ta samu shi ma mai ra’ayin karatun ne, idan ta samu ta gama, idan ya ce ba za ta yi aiki ba, shi kenan ta bari, dama dai ilimin an samu, sai ta nemi wata sana’a ko idan tana yi ta mayar da hankali sosai kanta.
Wacce shawara ki ke da ita ga mata masu zaman kashe wando?
Mata masu zaman kashe wando ko mata masu zaman kashe zani (dariya). To Allah ya sani wannan rayuwa ko da can da muka taso iyayenmu suna sana’oi. To sana’a dai a wurin mace dole ce, sai dai idan tana wani aiki na gwanmanti ne wannan da sauƙi. Amma yanzu da rayuwa ta yi tsada, maza ba za su iya yi su kaɗai ba. Rayuwar ta yi tsada, maza suna shan wahala, duk da dai mun san Allah ne Ya ɗora masu, kuma shi zai taimake su, to amma tadar rayuwar ta sa dole mace sai ta ɗan sa hannun ta a ciki ko yaya ne ta taimaka wa maigidanta a ciki. Kuma ba za a jira a ce sai randa mace mijinta ya mutu, ko auren ta ya mutu ne za ta fara sana’a ba. Ya kasance ta taso da son yin sana’ar tun kan ma ta yi auren ta koya. Kinga sai ta haɗa haske biyu ma, don wataƙila tana da ilimin addini wanda dole ne, sai ya zama tana da ilimin zamani da sana’a shi kuma saboda duniyar ta. Rayuwa ba ta da tabbas, idan muka kalli iyayen marayun nan da yawa idan ka bi labaran rayuwarsu da yadda rayuwa ta tsananta gare su sai kiga ya samo asali ne da rashin sana’a, ko rashin ingata sana’ar, ko rashin taimako da ba su samu ba daga mazajensu.
A kullum ina ba wa mata shawara da su yi sana’a, sannan maza su taimaka wa mata su yi sana’a, kuma kada a ɗora mata wani nauyi da ya fi ƙarfin sana’ar ta. Don haka ina ba wa mata shawara da su nemi sana’a, kuma kar su rena sana’ar.
Mun gode da lokacin ki.
Ni ma na gode ƙwarai. Allah Ya ƙara ɗaukaka Blueprint Manhaja Newspapers tare da dukkan ma’aikatansu, amin.
