Da Ɗumi-Ɗumi: Senegal ta lashe AFCON

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tawagar ‘yan ƙwallon ƙasar Senegal ta lashe kofin gasar ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025.

Hakan ya biyo bayan doke Moroko da ce 1 da nema a zangon ƙarin lokaci bayan shafe mintina 90 da ɗoriya ba tare da ɗayansu ya zura ƙwallo a raga ba.

Ɗan wasa Pape Gueye ne ya zura wata ƙayatacciyar ƙwallo a ragar Moroko, wanda hakan ya ƙayatar da masu kallo.

Wannan shi ne karo na biyu da Senegal ta lashe gasar a tarihinta tun bayan samun na farko a 2021.

By Babaji