
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya isa Conakry, Babban Birnin ƙasar Guinea domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu, a taron rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Mamady Doumbouya,
Za a gudanar da taron ne ƙarshen mako, a filin wasa na GLC Stadium, Nongo.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin Guinea da kuma mambobin ofishin jakadancin Nijeriya, gabanin bikin rantsarwar.
Hakan ya nuna kawo ƙarshen wa’adin mulkin soja na tsawon shekaru huɗu bayan babban zaɓen da aka gudanar a watan Disambar 2025.
Wakilcin da Mataimakin Shugaban Ƙasar ke yi ya jaddada rawar jagorancin Nijeriya a cikin ECOWAS musamman wajen goyon bayan dawowar Guinea kan tafarkin mulkin dimukraɗiyya, da inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali da ƙimar dimukraɗiyya a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Tinubu.
Kazalika, ziyarar, wata muhimmiyar manufa ce ta faɗaɗa kasuwanci da haɗin-gwiwar tattalin arziƙi tsakanin Nijeriya da Guinea, bisa ƙaruwar fitar da kayayyakin masana’antu da na noma daga Nijeriya zuwa ƙasar.
Shettima zai tafi Davos a ƙasar Switzerland, bayan Guinea domin halartar taron shekara-shekara karo na 56 na World Economic Forum (WEF 2026) da za a yi tsakanin ranakun 19 da 23 ga Janairu, inda zai tattauna da shugabannin duniya da masu zuba jari kan sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya, damar zuba jari, da rawar Afirka wajen gina tattalin arzikin duniya mai ɗorewa da haɗin-kai acikin al’ummominsu.


