
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla mabiya Ɗarikar Tijjaniya guda miliyan uku daga ciki da wajen Nijeriya ne suka taru a Katsina domin bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass na 2026 a ranar Asabar.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa an gudanar da taron ne a Filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Nyass.
Shugaban kwamitin shirya taron Sheikh Muhammad Hadi Balarabe ya ce sun samu aƙalla baƙi miliyan huɗu daga jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja da kuma ƙasashen Yamma da Arewacin Afirka.
NAN ya ruwaito cewa, kusan dukkan ɗakunan otal-otal ɗin da ke cikin garin Katsina sun cika da mahalarta taron. Haka ma gidajen ‘yan gari da ke da guraben kwana, lamarin da ke nuna karamcinsu ga baƙi.
Sannan, akwai waɗanda suka gaza biyan kuɗin otal wanda hakan ya sa suka kwana a filin taron duk da tsananin sanyi da ake fama da shi a garin.
Kazalika, an ga yadda cincirindon jama’a ya yi sanadin haifar da cinkoso musamman a yankin shataletalen WTC da titunan da ke kewayensa, lamarin da ya ba ƙananan ‘yan kasuwa damar samun gagarumin ciniki.
Da yake jawabi, Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi, ya yi godiya ga gwamnatin jihar Katsina bisa karɓar baƙuncin taron, yana mai addu’ar Allah ya samar da zaman lafiya da nasarori masu ɗorewa a jihar, arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.
