
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane guda uku da zargi ya yi ƙarfi akansu na alaƙa da kisan matar aure da ‘ya’yanta shida a Unguwar Ɗorayi Charanchi da ke jihar.
An yi nasarar haka ne sakamakon wani atisayen sirri da jami’an hukumar suka gudanar a dare ranar 17 ga watan Junairu da safiyar washe-gari.
A sanarwar da jami’in hulɗa da jama’arta, CSP Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an yi nasarar haka ne a bisa umarnin Sufeto Janar na rundunar, Kayode Egbetokun da kuma kulawar Kwamishinanta na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
A cewar hukumar, wani ɗa ga marigayiyar, ya amsa laifin kitsa yadda aka kai harin, wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta da ‘ya’yan nata.
Kakakin ya ƙara da cewa, tuni wanda ake zargin ya amsa cewa yana hannu a laifin sannan ya danganta kansa da wasu munanan hare-hare da kashe-kashe a cikin garin Kano.
Daga cikin ababen da aka gano daga masu laifin akwai kayan sawa huɗu da jini ya lalata, wayoyin hannu na marigayiyar, adda, gora da kuma wani adadi na kuɗi da aka yi zargin an sace su ne daga wajen da aka aikata ɗanyen aikin.
Kiyawa ya ƙara da cewa, ana gudanar da bincike domin gano ƙarin bayani akan al’amarin tare da kamo sauran masu hannu a ciki.
A ranar Asabar aka shiga har gidan matar mai suna Fatima Abubakar inda aka mata kisan gilla tare da ‘ya’yanta shida a Charanchi da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, lamarin da ya firgita jama’a musamman a arewacin Nijeriya.
Akan haka ne gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta yi alla-wadai da bayyana al’amarin a matsayin rashin imani tare da umartar a gaggauta farauto masu hannu aciki, kamar yadda Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana a wata takarda.
