Zawarci: Wasu mata na guje wa rabuwar aure ne don kada su rasa mu’amular aure – Yabi Muhammadu

Spread the love

“Mace a gidan miji sarauniya ce komai rashin daɗin gidan auren”

Daga AISHA ASAS

A ‘yan kwanakin baya can, wata baiwar Allah ta aiko da tambayarta a ƙarƙashin Dandalin Shawara wanda muka wallafa a shafin Iyali na wannan jarida.

A cikin bayanin ta, ta bayyana irin gallazawar da mijinta ke yi mata, tun daga ɓangaren abinci zuwa taɓa ɓangaren da mata da yawa ba sa iya jurewa wato neman mata, zuwa dai wasu ababe da na manta da su. Saidai a mamakin duk ta yi haƙuri da su, amma fa dalilin nata ne zai fi baka mamaki wato tana yin haƙurin ne don gujewa zawarci, wanda ta ce abu ne mai girma da ya fi wannan azabar da take ciki.

Na zaɓi inyi shimfiɗa da wannan ne domin fara darasin namu da ma’ana da ake yi masa a ƙasar Najeriya musamman ma a ƙasar Hausa.

Zawarci kalma ce da ake amfani da ita ga macen da ta yi aure, kuma ta rabu da mijinta, wato dai macen da aka saka ko kuma wadda mijinta ya mutu.

Kamar yadda bahaushe ya raba mace zuwa kashi biyu a sigar aure, wato budurwa wadda ba a taɓa aurenta ba, da kuma bazawara wadda ta yi aure ta fito, ko da sunan saki ko kuma mutuwar miji.

Kalmar bazawara kalma ce da mata da yawa ba su cika son a kira su da ita ba koda kuwa ba ƙarya aka yi masu ba, suna ƙyamatarta da har abin zai baka mamaki, duba da cewa hakan ma halastace, domin Allah da ya halasta aure, shi ne ya halasta saki, don haka bai zama laifi a Musulunci ba rabuwar aure, duk da cewa ba abinda ake so ba ne. Saidai irin yadda ake ƙyamatar zawarci ko bazawara har ya wuce sakin da dalilinsa.

Da wannan ne Blueprint Manhaja ta yi tattaki zuwa ga wata tsohuwa a Jihar Sakkwato don neman ƙarin bayani dangane da dalilin da ya sa macen da aka saka ba ta cika tagomashi ga al’umma ba, duk da cewa sau da yawa ba laifin ta ba ne.Tsohuwar mai suna Yabi ta bayyana mana cewa, “Ai ba kalmar ce abin ƙyama ba, abubuwan da ke tare da ita ta ɓangarori da yawa. Kinga dai da farko, ita mace budurwa da ba a kai ta ɗakin miji ba, kanta a rufe yake. Ba a samu kowa ya saki labule da ita ba, don haka su iyayenta ba su da tsoron ta san namiji da za ta iya neman sa ko amincewa da shi idan ya nemi lalata da ita. Saboda ba ta san wannan abu ba.

Ke ga ai idan aka kai budurwa ai gudun mijin take yi daga farko don ba ta san abinda yake zo mata da shi ba. Amma idan ta saba, za ki ga ita da kanta za ta dinga nema, don ya zamar mata tamkar abinci. To irin wannan na ɗaya daga cikin fargaba da iyaye ke da shi ga bazawara, domin ta san irin wannan nau’in abincin, kuma ta saba da shi, to idan ta dawo inda ba bu shi ai komai zai iya faruwa, amma fa ga wasu matan.

Da wannan ne iyaye da dama suka gwanmace ɗiyansu mata su zauna gidadajjen mazajensu ko da daɗi ko ba daɗi don gujewa su dawo gida a samu irin wannan matsala. Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ki ka ga wannan tsoron da iyaye ke yi ya fassaru a zukatan mutane ya sa tsoro a sunan zawarci ko bazawara.

Abu na biyu kuma shi ma yana da alaƙa da na farko, ita mace musamman wadda ke da sha’awar mu’amalar auratayya za ta shiga matuƙar damuwa idan aurenta ya mutu ba wai don son da takai ma mijinta ba, a’a, sai don rasa samun wannan abincin da ya kamata ta dinga samu duk dare. Da wannan ne za a iya samun ta shiga ƙunci mai yawa. Ke san ita mace aurenta ake yi ba ita ka aure ba, don haka sai ran da aka zo aka ce wance ina son ki in aure ki ne taka samun miji. Wannan ne zai sa ba zata iya fitar da kanta cikin wannan ƙunci ba sai ta samu wani mijin. Don haka wasu mata na gujewa rabuwar aure ne don kar su rasa mu’amallar aure.

Abu na uku kuma ga matan dai, ita mace a gidan miji sarauniya ce komai rashin daɗin gidan auren, in na ce sarauniya ba wai ina magana kan yadda shi mijin zai kula da ita ba, ina magana ne kan samun ɗaki ko gida da ta yi mallakin kanta. Idan za a yi abinci ita ce ke da haƙƙin dafa abinda ta ga dama, domin ita ce mai dafawar duk yadda gidan ya zama matuƙar dai an samu. Idan ma ba ta dafa ma, ita ɗin dai ce mai iko kan ɗan abinda aka samu na ci, ban sani ba ko kin fahimci gefen da na karkata, don na san wasu za su ce ai akwai wadda ko abincin ba ta samu, ko wadda zai dinga ba wa ɗan sulalla ya ce ta san yadda za ta yi da kanta. Duk yadda aka yi dai ita ce sarauniyar gida. Kuma shi namiji duk zafinsa ko rashin arzikin da yake wa matarshi akwai lokacin da yake rusuna mata ko ya so ko bai so ba. Don haka mace mai aure sarauniya ce duk matsin gidan auren.

To idan ta rasa aurenta ta rasa wannan sarautar. Za ta koma sai an yi a ɗan kwahwa mata a kwano. Idan ba ta yi sa’a ba ma ko ɗaki ita kaɗai ta zauna da ‘ya’yanta ba ta samu, saidai cikin ƙanenta ko ɗakin uwarta. Ke ga ko ta nan mace dole ta tsorace zawarci.

Ga kuma wata babba matsala wadda ita ce ta fi tsorata mata a rabuwar aure, ita ce barin mace da ‘ya’ya, ko a aikace ko a baki. Idan na ce a aikace akwai wasu mazan da tun matarsu na gidansu ta fahimci ‘ya’yan haihuwarsu kawai aka yi amma ba kula da su yake yi ba. Ba ruwanshi da sha’anin ‘ya’yansa. Ita ce dai kamo nan kamo can ta kula da su. (MANHAJA: Wannan ɗabi’a sau da dama takan zama sanadiyar yaɗuwar zina ta matan aure da sunan samun abinda za su ciyar da iyalinsu. Don haka ya kai maigida, kafin ka amince wa zuciyarka da bar wa matarka ragamar kula da yaran da ta haifa maka, ka fara da tunanin makomar abinda za ta iya yin don samar masu abinda suka yi buƙatu. Idan ka aminta da kowace ƙazanta za ta iya yi, wannan ba matsala, idan kuwa kana tunanin hakan a matsayin abin ƙyama, to ka yi saurin sauya tunani tun wankin hula bai kai ka dare ba.) To abinda zai zo wa macen da aka saka mai irin wannan mijin shi ne ‘ina ma gidan ya aka ƙarasa bare na taho na bar shi da yaran’ kinga ko ba ta da abin kula da su ko wurin zama mai kyau da zai ɗauke ta da ‘ya’yan za ta gwanmace ta taho da su idan ma wahalarce su yi tare a gaban idonta da ta bar su can ba ta san halin da za su shiga ba.

A gefe guda kuma wasu mazan musamman namu na Hausa sai kiga idan sun saki mace ba kunya za su faɗa mata ta tafi da ɗiyanta, in kuma ta ƙi kar ta yi masa ƙorafi idan ta ga ‘ya’ynata a halin da ba ta so, don zai kai su wuri kaza a riƙa masa, ko shi ɗin ba zai iya riƙa su ba, kuma ba zai yi aure ya ba matar ‘ya’yan da ba nata ba.

Da irin wannan barazana zai sa mace ko bata da abin yi sai ta kwaso ɗiya ta dawo zaman zawarci da su, kuma a irin wannan yanayi sai wadda Allah ya tsare, duba da irin halin rashin ɗa’a da wannan zamanin yake ciki, ba amcen ba namijin.”

Idan muka waiwaya kan sauran ƙabilu na ƙasar Najeriya za mu tarar da matsalolin na kama da juna saidai bambancin addini da kuma al’ada. A ƙasar Yarabawa, kalmar bazawara wata kalma ce da ake ƙamarta ba tare da dalili ba.

Idan miji ya mutu, wasu ɓangare na zargin matar da zama marar sa’a don haka za su ƙyamace ɗansu ya aureta don gudun shi ma ya mutu kamar tsohon mijinta. Masu sauƙi daga cikin al’ummar kenan, domin wasu za su zarge ta ne da zama ajalin mijinta kodai da hannunta, ko da aikinta ko kuma ta maitta ko tsafin da take yi ko kakanninta suka yi, ko wani alƙawarin da iyaye ko kakanni suka yi da aljannu kan bada mijin jikarsu a shekaru masu zuwa.

Idan kuwa macen rabuwa ta yi da mijin, akan ɗora kaso mai yawa na laifi kanta, inda wasu ke ganin halin mace ne ke sa a sake ta. Idan ta yi haƙurin da ya kamata ba yadda za a yi ya harzuƙa har ya sake ta. (Wannan ya tuna min da labarin wata mata da ‘yar uwarta ta taɓa bani, shekarun matar za su kai 50 ko sama ita wadda ake labarinta, ‘yar uwar ta ce, kusan shekaru 20 da aurenta da mijinta, amma a shekaarun 17 daga ciki a kullum ba abinda yake ba su ita da yaran da ta haifa masa na daga abinci face albasa. A kowace rana, ita ce za ta yi cefane daga sana’arta ta siyar da kifi, ta kawo, shi kuwa idan ya tashi daga kasuwa zai siyo masu albasa a matsayin cefane. Kamar yadda ‘yar uwar ta faɗa, ta ce ba ta taɓa yin ƙorafi ba, kuma a duk lokacin da za ta karɓi albasar daga hannunshi, sai ta duƙa, sannan ta yi godiya da cewa, “Mun gode, yadda ka ke kula da mu Allah Ya kula da kai.” Waɗannan kalamai nata na daga cikin abinda ke ba wa ‘ya’yanta haushi a lokacin da suka fara wayo, suna ganin yadda uwarsu ke wahala wurin ciyar da su da shi karan kansa mahaifin nasu, bayan kuma yana fita nema, amma duk da haka ta yi ta yi masa addu’a tare da girmamawa ba tare da ƙorafi ba. Wannan ita ce ɗabi’a ko tarbiyyar da iyaye Yarbawa suka yi wa ‘ya’yansu, wato darajar miji ba ta da kama, duk kuwa abinda zai yi maka na laifi ko rashin kyautawa).

Za mu ci gaba a mako mai zuwa…

By ukarofi