Ɗaliban kwalejin kimiyya sun halaka ɗan ajinsu a Yobe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani ɗalibin ajin ƙarshe (SS3) a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Potiskum da ke Jihar Yobe mai suna Hassan Ahmadu ya rasu a sakamakon lakaɗa masa duka da abokan karatunsa suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a jiya Lahadi acikin makarantar, wadda ke Ƙaramar Hukumar Potiskum ta jihar.

A cewar wata majiya daga gidan su mamacin mai kimanin shekaru 17, tuni aka yi jana’izarsa a ranar da abin ya faru a garin Gadaka da ke Ƙaramar Hukumar Fika a jihar.

An ruwaito cewa, wasu ‘yan ajinsu ne suka farmaki shi bisa wasu dalilai da ba a kai ga tantance su ba daga ɓangaren hukumomi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya shaida wa manema labarai cewa jami’ansu sun fara gudanar da bincike akan dalilan da suka sabbaba mutuwar ɗalibin.

Wani malami da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa ‘yan jarida cewa Hassan ya riƙa fuskantar tsangwama na wani lokaci, inda a ranar Lahadin ya (Hassan) nemi da su daina takura masa, amma duk da haka sai da suka farmake shi, inda daga bisani ya rasu.

Ya ƙara da cewa, bayan harin hukumar gudanarwar kwalejin ta damƙa waɗanda ake tuhuma da hannu a laifin ga ‘yan sanda.

By Babaji