
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dattawan ta sanar da cewa za ta gudanar da zaman gaggawa ranar Talata, 10 ga Fabrairu domin tattauna batun kudirin gyaran dokar zaɓen da ya janyo cece-kuce a faɗin Nijeriya.
Rahotanni sun nuna cewa an kira wannan zaman ne sakamakon ƙorafe-ƙorafe da matsin lamba daga jama’ar ƙasa musamman dangane da batun tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura, wato “electronic transmission of results”.
Za a gudanar da zaman neda misalin ƙarfe 12 na rana inda aka buƙaci kowane sanata ya halarta.
Mutane da dama na ganin matakan ƙin amince wa wajibcin watsa sakamakon zaɓe ta na’ura na daga cikin abin da ya haifar da koma baya ga kiyaye gaskiya da adalci a babban zaɓen 2023.
Ana sa ran zaman zai ƙunshi duba ƙudirin da kyau tare da daukar matakan da suka dace domin kwantar da hankalin jama’a da kuma kare sahihancin tsarin dimukraɗiyya a Nijeriya.
