An fara zanga-zangar neman wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Masu zanga-zanga na taruwa a Abuja domin gudanar da gangamin “Occupy National Assembly” don nuna adawa da ƙin amincewar da Majalisar Dattawa ta yi kwanan nan game da tura sakamakon zaɓe ta na’ura.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun yi cincirindo a wurin, inda aka jibge na hukumomin ‘yan sanda, sojoji da na Cibil Defense (NSCDC).

Zanga-zangar ta biyo bayan matsayar Majalisar Dattawa ta ƙin amincewa da wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura.

A ranar Laraba, an ruwaito cewa Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da gyaran da aka gabatar ga Sashi na 60, ƙaramin sashe na 3 na Dokar Gyaran Zaɓe, wanda zai tilasta yin tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki.

A lokacin da ake kawo wannan rahoto, masu zanga-zangar sun fara tafiya daga Babban Sakatariyar Tarayya (Federal Secretariat) zuwa ƙofar Majalisar Tarayya.

Zuwa yanzu dai masu zanga-zangar na ƙara nausawa zuwa harabar majalisar ɗauke da alluna masu rubutu na neman janye matsayar, abin da suka kira yunkurin murɗiya a zaɓen 2027 da ke tafe.

By Babaji