Ramadana: Gwamnan Kaduna ya buƙaci malamai da gidajen jarida su faɗakar akan muhimmancin zaman lafiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya buƙaci malaman addinin Islama da kafafen yaɗa labarai da na sadarwar zamani da su yi amfani da watan Ramadan da ke tafe a matsayin wata babbar dama ta ƙarfafa kira da zaman lafiya, haƙuri da haɗin kan ƙasa.

Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na kafin Ramadan na 2026 da ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya a babban hedikwatarta da ke Kaduna.

Gwamnan wanda Sakataran Gwamnatin jihar, Dakta Mu’azu Meyare ya wakilta, ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziƙi, tsaro da zamantakewa da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu sun ƙara ɗora nauyi a wuyan malamai da kafafen yaɗa labarai wajen jagorantar al’umma da hikima, ladabi da tausayi.

Don haka ya yi kira ga malamai da su tabbatar da cewa darussan tafsiri da sauran shirye-shiryen wayar da kai na ramadan suna ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, adalcin zamantakewa da kula da marasa galihu.

Haka kuma, ya ce ramadan wata ne mai tsarki da rahama, tarbiyya inda ya buƙaci al’umma da su yi amfani da lokacin wajen ƙarfafa dabi’un sadaka, kishin ƙasa da addu’o’i ga ƙasa da shugabanninta domin samun ci-gaba mai ɗorewa.

Kazalika, ya bayyana cewa addu’o’i na gaskiya a wannan wata mai albarka suna da muhimmiyar rawa wajen warkar da ƙasar daga mikin ciwon da samu na rashin tsaro.

Har ila yau, ya kirayi gidajen rediyo, talabijin da kafafen sada zumunta na zamani da su kiyaye ƙa’idojin ƙwarewa da ladabi wajen watsa tafsiri da sauran shirye-shiryen addini, yana mai gargadin lallai ne a guji saƙonnin da ka iya tayar da fitina ko rarrabuwar kai acikin al’umma.

By Babaji