
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa Nijeriya na buƙatar ƙarin sojoji da haɗin-gwiwar tsaro da Amurka domin yaƙar ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a arewacin Nijeriya.
Remi Tinubu ta kuma bayyana harin Amurka na ranar Kirsimeti a matsayin albarka ga Nijeriya, sannan ta bayyana fatanta na samun ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
A lokacin da ta kai ziyara Amurka, tsohuwar sanatar daga Legas ta yi tsokaci akan hare-haren sojojin Amurka a Nijeriya guda biyu da aka ƙaddamar da su ta sama a Sakkwato, waɗanda aka nufi wasu wuraren ‘yan ta’adda da su.
Haka kuma, ta halarci taron addu’ar ƙasa tare da Shugaban ƙasar, Donald Trump, wanda shi ya umarci a ƙaddamar da hare-haren a wani yunƙuri na yaƙi da ta’addanci.
A cewar Uwargidan Shugaban Ƙasar, Amurka ta samar wa Nijeriya sauƙi musamman a wannan lokaci da mutane da dama ke rasa rayukansu a sanadiyyar hare-haren ‘yan ta’adda, tana mai cewa gwamnatin tana ƙoƙarin magance matsalar.
Harin ranar Kirsimetin shi ne na farko da Amurka ta ƙaddamar a Nijeriya tun bayan ayyana ƙasar a matsayin wadda ake da damuwa akanta da Trump ya yi watanni kaɗan da suka gabata.
Bayan nan Shugaban Amurkan ya tura wata tawagar sojojin zuwa Nijeriya a wani yunƙuri na daƙile ayyukan ‘yan ta’addar da suka addabi sassan ƙasar.
