“Rashin sana’ar yi ga mace musamman matar aure ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba”
Daga AYSHA ASAS
Hajiya Fatima Umma Salisu Gwadabe, mace mai neman na kanta a ɓangaren sana’ar sayar da abinci, wadda ta kafa yara kuma ta koyar da su sana’ar don su ma su dogara da kansu. A wannan makon jaridar Blueprint Manhaja ta samu damar tattaunawa da ita don jin wasu batutuwa da suka shafi irin sana’ar da yadda sana’ar ke da tasiri a rayuwar matan aure. Sannan mun taɓo ɓangaren rayuwarta. Kuma za ku ji irin shawarwarin da ta ba wa mata musamman masu aure. Idan kun shirya, zan ce a sha karatu lafiya.
MANHAJA: Mu fara da jin taƙaitaccen tarihinki.
GWADABE: Sunana Fatima Umma Salisu Gwadabe, an haife ni ranar 29 ga watan Yuni 1977. Na yi makarantar nursery a ƙueen Amina Nursery School, Hadejia Road a garin Kano, daga nan na tafi makarantar firamare ta Aliyu Ibn Abi Talib daga 1984 zuwa 1989, na sauke Al-ƙur’ani mai girma ina da shekara 11 a duniya kafin na je JSS 1. Daga nan na je sakandare ta Kano State Foundation Girls daga 1989 zuwa 1991. Bayan nan kuma na tafi makarantar sakandare ta gwamnati da ke Taura a Jihar Jigawa daga 1991 zuwa 1994. Sai kuma na shiga Kano State College of Arts Science and Remidials CAS a 1995. Daga baya kuma na tafi Jami’ar Bayero da ke Kano inda na yi karatun difloma a ɓangaren ilimi.
Wacce irin sana’a ki ke yi a halin yanzu?
To ni dai sana’ar da kowa ya sanni da ita, ita ce catering, wato sana’ar abinci kala-kala.
A wannan zamani da ake ciki, ki na ganin zaman mace ba sana’a zai haifar ma ta ɗa mai ido?
Gaskiya mace ta zauna haka siddan babu wata sana’a akwai matsala, domin ba kowace matsala ba ce maigidanki zai magance miki, to idan kina sana’arki ko ‘yar yaya take za ta taimake ki da ke da ‘ya’yanki, kuma har ki taimaka ma sa da sauran ‘yan uwanki da iyayenki. Saboda haka rashin sana’ar yi ga mace musamman matar aure ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba.
A matsayinki ta mace kin samu ƙalubale a ɓangaren sana’arki?
Gaskiya ba sosai ba, duk da akwai ɗan kishi da ake samu a cikin sana’ar, saboda mun yi yawa. Amma Alhamdu lillah, duk da haka ya danganta da yawan kwastomomin ka, to gaskiya ni ina da kwastomomi daidai gwargwado.
Waɗanne nasarori ki ka samu zuwa yanzu?
Kai nasarori ai ba su ƙirguwa, domin wannan sana’ar ta yi min riga da wando. To gaskiya Alhamdu lillahi.
Iyali fa?
Ina da aure da ‘ya’ya guda huɗu, uku maza, ɗaya mace, sai kuma ‘ya’yan ‘yan uwana da suke tare da ni.
Wane kalar kaya ki ka fi so?
Gaskiya na fi son dogayen riguna.
Wane abinci ki ka fi so?
Na fi son wake da shinkafa.
Me ke saurin ɓata maki rai?
Ba na jin daɗi a ce na yi yi magana ba a fahimce ni ba, ko kuma a fassara magana ta da wata manufa wadda ba daidai ba.
Me ke birge ki?
Ina so in ga ana zumunci, gaskiya abin yama birge ni.
ƙasashe nawa ki ka taɓa ziyarta?
Na je ƙasar Saudiyya, Dubai, Egypt, London da kuma Ethiopia.
A cikin ƙasashen da ki ka ziyarta, wacce ƙasa ki ka fi so?
A cire ƙasar Saudiyya wadda kowane Musulmi yake kwaɗayin zuwa. Gaskiya na fi son Egypt, ina son ƙasar sosai, a duk lokacin da na je ina samun natsuwa tun daga 2018 da na fara zuwa ƙasar. Garin da mutum zai je ya huta, su na birge ni wajen karatun Al’ƙur’ani, musamman ma ‘ya’yan ‘yar uwa ta da na ke zuwa wajen su a can, su na da wani matsayi sosai a cikin zuciyata, kuma su na sani kewar ƙasar sosan gaske.
Wacce shawara za ki ba wa mata masu zaman kashe wando?
Mata waɗanda ba su da sana’ar yi ina ba su shawarar da su farka, su tashi tsaye don neman na kansu. Kada ki ce sai kina da jari mai yawa, a’a ki duba sana’ar da ‘yan kuɗaɗen da ke hannunki za su iya yi miki, sai ki fara a hankali a hankali, sai ki ga kin miƙe, amma komai ɗan haƙuri ne, idan ki ka bi a hankali kuma ki ka tattala sai ki ga kin kai ga taimakon har waɗansu, ba ma ke kaɗai ba.
Shin a ganin ki tarbiyyar ‘ya’ya wa ya kamata ya tsaurara tsakanin uwa da uba?
Har da uba, saboda idan ki ka lura ‘ya’ya sun fi tsoron iyayensu maza, kuma uwa akwai tausayi tarbiyyar yanzu kuwa sai an jajirce.
To amma me ya sa a duk lokacin da yaro ya lalace sai a ɗora laifin akan uwarsa. A ta ki fahimta me ya sa ake ɗora mata laifi?
Gaskiya ni dai ina danganta shi da raunin mu da kuma son kai, tun da kin ga ko a zamantakewar aure an fi ɗora wa mata laifi, wanda hakan bai kamata ba, namiji koyaushe yana ganin ai shi fita nema yake, saboda haka wannan akan ki yake. To batu na gaskiya shi ya kamata ya fi sa ido.
‘Ya ya aka ce rahma ne, sai dai a wannan zamani da yawa a iyaye maza na kyamatar tara su, shin a na ki nazari me ya janyo hakan?
Abin da na fuskanta shi ne gaskiya maza a wannan zamani ba sa son ɗaukar ɗawainiyar su, kodayake ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Ga kuma yadda yanayin rayuwa take a yanzu.
Mene ne matsayin da girki ke da shi a zamantakewar aure?
Girki na da muhimmanci sosai gaskiya, abu ne da za ka yi alfahari da shi sosai idan ka iya, kuma iya girka abinci mai daɗi yana taimaka wa zaman lafiyar aure. A taƙiice Iya abinci ne sinadarin riƙe maigida.
Shin namiji ɗan goyo ne?
(Dariya). Sosai ma kuwa! Tun da yana taka babbar rawa a aure.
To Hajiya mun gode ƙwarai.
Ni ma na gode ƙwarai.
