Za a kammala aikin tagwayen hanyar Sokoto-Gusau-Funtua zuwa Zaria a shekarar 2028 – Goronyo

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin tarayya ta ce, za a kammala aikin tagwayen hanyar Sokoto-Gusau-Funtua zuwa Zariya a shekarar 2028.

Karamin Ministan ayyuka, Bello Mohammed Goronyo ya yi wannan tsokaci a wata hira da manema labarai a Garin Bungudu hedikwatar ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara a yau Lahadi.

A cewar sa, ziyarar gani da ido na gina hanyar ta Sokoto-Gusau-Funtua zuwa Zariya wanda ma’aikatar sa ta yi, ya biyo bayan umarnin ministan ayyuka, David Umahi, da nufin duba ayyukan da ‘yan kwangilar da ke kula da aikin ke yi da kuma tabbatar da ayyukan cikin sauri da inganci.

Ya ce idan aka kammala aikin, zai inganta ci gaban tattalin arziki na jihohi huɗu na Kaduna, Katsina, Sokoto da Zamfara.

A cewarsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙuduri aniyar tabbatar da kammala aikin kamar yadda aka tsara kuma bisa yarjejeniyar kwangilar.

Goronyo ya nuna rashin gamsuwa da jinkirin da kamfanin Triacta ya yi, na Kimanin kilomita 37 da Kamfanonin ke gudanarwa wanda a cewarsa kwangilar ta kai kashi 16 cikin 100 kacal na kammala ta.

Ya gargaɗi dukkan kamfanonin kwangilar da ke kula da gina tagwayen hanyar Sokoto zuwa Zariya da su tabbatar da ayyuka masu inganci kuma bisa yarjejeniyar kwangilar.

Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan gina hanyar ta Zaria-Funtua -Gusau zuwa Sokoto, yana mai cewa zai taimaka wajen haɗuwar jihohi huɗu da suka ƙunshi Jihar Kaduna, Katsina, Sokoto da Zamfara wajen inganta harkokin sufuri.

By ukarofi