Yadda badaƙalar Walida Abdulhadi da Ese Oruru suka yi kamanceceniya

Spread the love

Bai kamata a bambanta shari’ar Walida Ese ba, inji masu sharhi 

Daga AISHA ASAS

Rayuwar ‘ya mace rayuwa ce mai rauni, wanda hakan ya sa a duk tsayin rayuwarta tana yin ta ne a ƙarƙashin kulawar wani. Sai dai idan na ce kulawar wani ba Ina nufin kowa ya tara hannu za ta faɗa ba.

Ita mace kamar yadda take da rauni haka take da mautuƙar hatsari idan ta samu kanta a inda ba haka tsarin addini ko al’ada ya tanada ba. A cikin kowane yare ko addinan da muke da su manya a nan Najeriya, babu wanda ya amince da mace ta yi rayuwa a kara zube. Ita ce halitta guda ɗaya da ake ba wa muhimmanci da tarairiya fiye da kowace.

Mace tana da daraja matuƙa a mafi yawa daga cikin addinai da kuma al’adu, don haka aka tsara mata rayuwa tun tana ƙarama har zuwa girma.

Idan zan yi magana da bakin malam bahaushe da kuma addinin Musulunci, mace mutum ce mai daraja da ƙima a cikin sa, musamman ma idan ka fi duba ta ɓangaren addinin Islama.

Lokaccin da aka haifi mace, kulawarta na hannun iyayenta ko makamantansu idan ƙaddarar rabuwa ko mutuwa ta auku. Idan ta isa aure, aka ce a yi taka-tsan-tsan wurin ganin an aurar da ita ga mutumin kirki. Kamar yadda Hadisi ya bayyana cewa, Manzon rahma ya ce, “…..idan ku ka samu wanda ku ka yarda da addininsa da halayyarsa, to ku ba shi aure………..”

Idan mace ta yi aure, Musulnci ya tsara mata rayuwa a gidan aure, da yadda za a kula da ita da kare martabarta da mutuncin ta. Daga ƙarshe kuwa idan aka waye gari babu mijin, to idan tana da sauran ƙurciya za a ba ta shawarar ta yi aure don komawa ƙarƙashin kulawar da ta dace da ita. Idan kuma ta kai girma kuma ba ta sha’awa ko ta kai shekarun da ba ta muradin yin aure, to kulawarta za ta koma hannun ‘ya’yanta maza da ta haifa.

Abin lura a nan dai shi ne rayuwar mace gaba ɗaya a hannun wani mutum da aka zaɓar mata take, don haka yayin da wannan rayuwar tata ta sha kwana zuwa ga wata hanya da ba a sani ba, tsoro da fargaban makomarta zai dasu a zukatan waɗanda suke da iko a kanta.

A wannan makon shafin Gimbiya zai yi duba ne kan rayuwar matashiya Walida Abdulhadi Ibrahim wadda lamarin ta ya zama a bin taɓa zukatan mutane da dama tare da saka tsoro ga iyaye masu matasan ‘ya’ya irin ta, domin duk abinda ya taɓa gira zai iya taɓa ido.

Lamarin Walida Abdulhadi Ibrahim ya zama ɗaya daga cikin shari’o’in da suka fi ɗaukar hankalin jama’a a ‘yan shekarun nan, ba wai saboda ruɗani da ya dabaibaye lamarin ba kaɗai ba, har ma da dalilin tarin tambayoyin da suka dasu a zukatan mutane musamman ma iyayen ‘ya’ya mata kan tsaro ga ‘ya’ya mata. Makomar ‘ya’yansu mata da irin barazanar da za su iya fuskanta a nan gaba, tare da tambayar da ta fi tsorata iyaye wato waye zai ba wa ‘ya’yansu tsaro? Idan har ‘yan ta’adda za su sace masu ‘ya’ya, wurin wa za su juya don neman ‘yancin ‘ya’yansu? Ina ce hukuma ce, to idan hukumar ta zama abin zargin su ta wannan ɓangaren ina za su juya?

Yadda ake aiwatar da doka a ƙarar nan mai cike da rarrabuwar ra’ayi abin tada hanakali ne ga duk wani mai hanakali.

Tun bayan ɓacewar Walida a shekarar 2023 daga Hadejia ta Jihar Jigawa, lamarin da ya kasance cikin duhu a tsawon lokaci mai tsayi, kafin daga bisani ya ɓullo da sabbin bayanai da suka tayar da ƙura a fagen shari’a tare da saka zargi a zukatan al’umma, wanda ya bar muhawara mai zafi a tsakanin jama’a.

Sauyin da ya fi ɗaukar hankali shi ne miƙa kulawar Walida daga hannun Hukumar farin kaya wato DSS zuwa ga Gwamnatin JIhar Jigawa a satin da ya gabata, inda Gwamnan Jihar, Umar Namadi ya karɓi alhakin kulawa da ita a hukumance. An gudanar da wannan miƙa ikon ne a Brinin Tarayya Abuja.

Wannan mataki kawai zai iya ƙara tsorata al’umma domin ganin hakan kawai zai iya karkatar da tunani l kan cewa wannan batu ya wuce iyakar binciken tsaro kawai, akwai yiwar abinda mutane da suke zargi yana da ƙamshin gaskiya, wato ‘ya’yansu ba su tsira ba har a hannun hukuma, domin batun ya koma doguwar shari’a da watakila wani ɓangare na son fere biri har wutsiya.

Gwamnan ya bayyana Walida a matsayin “ɗiyar Jigawa” yana mai jaddada cewa gwamnati za ta tabbatar da tsaron ta da walwalarta, sannan kuma za ta bar duk wani hukunci a hannun kotu. Haka kuma ya tabbatar da cewa, jaririyar da da ita Walida ta haifa a watan Nuwamba(wadda ake zargin ta haife ta ne da wani jami’in hukumar farin kaya) za ta kasance ƙarƙashin kulawar gwamnati har sai an kammala dukka matakan shari’a.

Na san wasu daga cikin masu karatu sun ji labarin ne daga sama, wanda hakan ya hanasu sanin asalin haƙiƙanin abinda ya faru tun daga ɓacewar Walida Abdulhadi Ibrahim kawowa yanzu, don haka za mu dan yi ribas don a fahimci lamarin sosai.

A cewar ahalinta, Walida ta ɓace ne a shekarar 2023, lokacin da take ɗaliba a sakandare. Mahaifinta ya bayyana cewa ranar da ta ɓace, ya tafi gona kamar yadda ya saba, ya dawo ya tarar da kowa cirko-cirko ba a san inda Walida take ba.

An shiga nema cikin Hadejia har da makwabta, amma ba wani sahihin labari da ke iya nuni da inda take.

Tsawon shekaru biyu ahalin suka yi cikin baƙin ciki da jimame, a wata majiya ma aka ce a cikin shekarar ta biyu, mahaifin nata ya yanke shawarar yi mata zaman makoki don tsayin lokacin da nuna masu yiwar ta rasu ne.

Zancen iya bayyana halin da wannan zuri’a suka shiga a wannan lokaci ba abu ne da zai yiwu a rubutu ba kuma ba abu ne da wanda bai ɗanɗana zai iya misaltawa ba, domin lokuta da dama iyaye sukan ce gwara ‘ya’yansu su mutu da su ɓata, domin idan mutuwa ce sai su yi kuka, su bar wa Allah. Amma ita ɓata babu ranar da za ka iya haƙura da ita, a kullum sa ran ganin ɗan naka ka ke yi, hakan zai hana raɗaɗin sauƙi.

A watan Disamba na shekarar 2025 ne mahaifin Walida ya samu kira ta wayar hannu cewa Walida tana nan a raye, kuma tana Abuja, har ma ta samu ƙaruwa, uban ya zama kaka, wato ta haifu, wanda hakan ba wani dogon tunani za ka amince a can ta same shi, kuma ta haife shi. Wannan saƙoni biyu da suka zo a lokaci guda sun zo da mabambantan matsayi a zuciyar iyaye da ‘yan uwan Walida. Wanda hakan ya jefa su a dogon nazari da bincike kan ya hakan ta kasance, wake da laifi kuma me ya sa?

Ba jimawa muka samu rahotannin shigar da ƙorafi da iyayen Walida suka yi, inda suke zargin wani jami’in farin kaya da hannu a tsarewar ta, da kuma aikata laifuka da suka shafi take haƙƙinta.

Hukumar ta farin kaya ta bayyana cewa, jami’in da ake zargi yana tsare, kuma ana gudanar da bincike a kansa, tana mai tabbatar da duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada. Hakan kuwa na nuni da akwai ɗan ƙamshin gaskiya akan zargin na iyayenta.

A nata ɓangaren, Walida ta bayyana a wata fira da aka yi da ita cewa, tun a farko wata mata ce ta sace ta tare da gallaza mata, daga bisani ta kai ta Abuja. Ta kuma ce tana tsoron komawa gida, lamarin da Hukumar DSS ta ce ya sa aka ci gaba da riƙe ta don kare lafiyarta.

Wannan saɓani tsakanin iyayen Walida da hukumar ya ƙara rikitar da al’amarin, musamman ganin cewa wata kotu a Jigawa ta bayar da umurnin a miƙa ta ga iyayenta, yayin da hukumar DSS ta bijirewa umurnin, inda ta ce tana ƙarƙashin dokar kariya ne har sai an kammala bincike.

Babban lamarin da ya ƙara jefa shari’ar cikin ƙarin rikici akwai zancen shekarunta, wanda iyayenta suka ce tana da shekaru 16 a lokacin da ta ɓata, hakan na nufin tana ƙarƙashin dokokin kariyar yara, ma’ana shekarunta ba su kai na yanke hukuncin kanta ba. Saidai hukumar ta DSS ta musanta hakan inda suka gabatar da hujjar da ke nuna an haife ta ne a ranar 7 ga watan Fabrailu, na shekarar 2024, wanda hakan ke nufin baliga ce ko da aka ce ta ɓata. Ma’ana dai suna son nuna koda Walida ta ɓata tana da damar yanke wa kanta hukunci a shari’a, na daga inda take son zama zuwa wanda za ta zauna da shi har ma da ikon bijewa zaɓin iyayenta.

Wannan bambanci ba ƙaramin ruɗawar zai yi ba a gaban kotu, domin idan har maganar iyayen Walida ce kawai aka tabbatar to fa koda Walida ta ɓata yarinya ce ƙarama da ba ta kai shekarun ‘yanci ba a hukumnce, don haka dokokin kariyar yara za su yi tasiri kai tsaye, kuma duk wani zargi na sacewa ko riƙewa idan ya tabbata zai zama laifi mai tsanani.

Idan kuma baliga ce kamar yadda hukumar DSS ke iƙirari, za a yi la’akari da ‘yancinta na zaɓin rayuwa, saidai hakan ba yana nufin ba za a bincike zarge-zargen da aka yi ba.

ƙungiyoyi da dama musamman na mata Musulmai kamar FOMWAN (Federation of MUslim Women’s Association in Nigeria), da MURIC (Muslim rights Concern) sun buƙaci a bi umurnin da kotu ta bayanr tare kuma da tabbatar da an kare haƙƙinta ba tare da son rai ba.

Haka kuma ƙungiyar lauyoyi mata wato FIDA ta shiga lamarin inda ta nuna goyon bayanta ga gaskiya kan lamarin Walida da kuma kira da kada a saka son rai a cikin shari’ar wanda hakan na nufin tauye haƙƙin ita yarinyar.

Wannan lamari na Walida ya tado da tsoron tabo, na shari’ar Ese Oruru, wadda a baya ita ma aka yi mata kwatankwacin abinda aka yi wa Walida. Masu sharhi da dama sun alaƙanta lamarin inda suka ce ba abinda ya kamata ya bambanta shari’ar Ese Oruru da Walida Abdulhadi Ibrahim, inda suka nemi a yi amfani da mizani iri guda wajen tabbatar da adalci, ba tare da la’akari da addini ko matsin lamba daga jama’a ba.

Saidai a ɓangaren hukumar DSS, Darakta Janar na Hukumar ta farin kaya, Adeola Oluwatosin Ajayi, ya yi kira da a kauce wa jefa lamarin cikin rikicin addini ko ƙabilanci. A cewarsa, babban abin da ya kamata a fuskanta shi ne tsaro da makomar Walida. Kuma a bar doka ta yi aikinta.

A ma’auni na hankali, wannan lamari ya zama babbar jarrabawa ga ƙasa baki ɗaya. Yadda za a warware shi zai nuna yadda Najeriya ke ɗaukar ababen da suka shafi ‘ya mace da muhimmaci ko akasain haka. Kuma shari’ar za ta ɗora haƙƙin ɗan ƙasa kan mizani da kuma ƙarfin ikon da hukumomi suke da shi.

By ukarofi