Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A saƙon sa na bikin ranar Mata na duniya Malam Dikko Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa rayuwa, mutunci da ‘yancin tattalin arzikin mata a faɗin jihar.
Ya bayyana cewa zuba jari ga mata tamkar zuba jari ne ga al’umma baki ɗaya. Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da wannan kuduri ta hanyar ɗaukar matakai masu amfani a aikace.
“Idan ka tallafa wa mata, al’umma baki ɗaya za ta amfana. Wannan shi ne ma’anar taken bana ‘Ba da domin Samu’. A Jihar Katsina ba kawai magana muke yi ba, muna aiwatar da shi a aikace.”inji Malam Dikko.
Gwamnan ya kuma bayyana wasu daga cikin shirye-shiryen tallafawa mata da gwamnatinsa ta aiwatar. Ya ce a watan Janairun 2026, gwamnatin Building Your Future ta bai wa mata 14,450 daga ƙananan hukumomi 34 na jihar tallafi domin bunƙasa sana’o’insu.
Kowacce mace ta samu tallafi gwargwadon sana’arta, ciki har da kayan aiki, injinan niƙa, firiza, kaji da abincinsu, hatsi, kayan ɗinki, kayan kwalliya da kuma kuɗi.
Gwamnan ya ƙara da cewa, “Makonni biyu kafin wannan, ‘yan mata 1,000 masu tasowa sun samu tallafi a ƙarƙashin wannan tsari. Haka kuma a shekarar 2025, fiye da mata 36,000 a faɗin jihar sun amfana da shirye-shiryen tallafawa daban-daban.”
A yayin taron “Where Influence Meets Investment” Summit da aka gudanar a watan Janairu, Gwamna Raɗɗa ya sanar da ware ƙarin Naira miliyan 500 domin tallafawa mata ‘yan kasuwa, domin bunƙasa sana’o’in, ƙwarewa da faɗaɗa kasuwanninsu.
Har ila yau, ya bayyana cewa Jihar Katsina ta ware Naira biliyan huɗu a kasafin kuɗin shekarar 2026 a matsayin tallafin hadin gwiwa ga shirin gwamnatin tarayya na Nigeria for Women Project, wanda ke ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen bunƙasa tattalin arzikin mata a Najeriya.
Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya kawai wajen raba kayan aiki da kuɗi ba, sai ta tabbatar da cewa kowace mace a Katsina tana da ƙwarewa, dama da tallafin da za su taimakawa mata wajen gina rayuwa mai ɗorewa.
A wannan rana ta mata ta duniya, Gwamnan ya buƙaci mata a faɗin Jihar Katsina da su ci gaba da ɗaga kai, su kuma yi amfani da damar da gwamnatinsa ke samarwa domin inganta rayuwarsu.
Dikko Raɗɗa ya taya dukkan mata a Jihar Katsina da ma duniya baki ɗaya murnar ranar mata ta duniya.
