
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Ƙwararru ta Iran, ta sanar da naɗa Mojtaba Khamenei a matsayin magajin mahaifinsa, matakin da ake ganin zai ƙara tsananta tashin hankali tsakanin Iran da kuma Amurka da Isra’ila a ɗaya ɓangaren.
A cewar gidan talabijin na Iran da kuma rahotannin duniya, an ɗauki wannan matakin ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar babban ƙalubalen yaƙi tun bayan fara harin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar tun ranar 28 ga watan Fabrairu
Mojtaba Khamenei, wanda ke da tasiri sosai a cikin tsarin soja na ‘Islamic Revolutionary Guard Corps’ (IRGC), ya zama mutum na biyu da ya riƙe wannan matsayi tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.
Hakan na zuwa ne yayin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa, duk wanda aka zaɓa ba tare da amincewarsu ba, ba zai daɗe a kan karagar mulkin ƙasar ba.

