
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ta gano wasu gidaje a ƙasar Misra da aka danganta su da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i.
Gano kadarorin na daga cikin ɓangarorin binciken da hukumar ke yi akan wa’adin mulkin El-Rufa’i a lokacin da yake gwamnan Kaduna.
Cikin ababen da aka gano akwai manyan rukunin gidaje guda uku da gidaje shida, waɗanda aka ce a unguwanni masu alfarma suke da yankunan Cairo, Babban Birnin ƙasar.
A cewar wani bincike da TheCable ta wallafa, an sayar da gidajen ne, waɗanda suke Arabilla Estate da Banafsik Estate a tsananin Dala miliyan 1 da zuwa Dala miliyan 1.3.
Sai kuma na Cairo Festival City, waɗanda aka musu farashi akan Dala 500,000 kowannensu.
Wasu majiyoyi da ke bibiyar binciken gwamnatin El-Rufa’i sun bayyana cewa an mallaki gidajen ne daga shekarar 2021 zuwa 2023 a lokacin da yake gwamna.
Ga bayanin gidajen da wuraren da suke kamar yadda jaridar IntelRegion ta ruwaito “..one villa at Arabilla estate, 5th settlement area in Cairo, another villa at Banafsik estate, 1st settlement area, New Cairo, and another villa in Oriana II, New Cairo (near American University).”
Sauran sune: “four apartments in Cairo Festival City and two more in Oriana Estate, New Cairo”, ƙamar yadda jaridar ta ruwaito.
