
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya (PDP) na dab da sake rasa gwamnoni guda biyu yayin da na Jihar Bauchi, Bala Mohammed da takwaransa na Oyo Seyi Makinde suke shirin barin jam’iyyar kafin watan Afrilu.
Rikicin shugabanci da ke cikin jam’iyyar na cigaba da faɗaɗa wanda ya sa jiga-jigan cikin ke cigaba da ficewa zuwa mai mulki ta APC.
Tun daga babban zaɓen 2023, an samu aƙalla gwamnonin PDP 9 da sanatoci 19 da ‘yan majalisar tarayya 47 da suka suya sheƙa daga jam’iyyar saboda abin da suka kira da rikicin da kaa gagara magancewa.
Wata majiyar mai ƙarfi ta bayyana cewa, yayin da Bala Mohammed ke shirin shiga APC, Gwamna Makinde ya kammala shirin koma wa ADC.
Babu shakka akan cewa ‘yan siyasa da dama na halin matsi akan sauya sheƙar jam’iyyu kafin Afrilu, bisa la’akari da tsare-tsaren saboda jaddawalin babban zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe INEC, ta fitar.
Jam’iyyar PDP ta cigaba da fuskantar rashin mambobinta zuwa APC da wasu jam’iyyu. ‘Yan tsagin Ministan Abuja Nyesom Wike da Turaki suna cigaba da ikirarin jagorancinta.
