Kin iya kunu? (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku mai albarka na zamantakewa mai zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja.

Da farko ina taya ku murnar shigowar watan azumi na Ramadan watan rahama watan yafiyar zunubai. Dafatan za mu dage da zikiri da ambaton Allah da istigifari don rabauta da wannan gwaggwavan lada. A makon da ya gabata mun fara bayani a kan sirrin madafi. Wato a game da tambayar mata sun iya kunu? Ba kunun kaɗai ba, kin san sirrin tukunya?

A makon da ya gabata mun fara yi muku bayani a kan hanyoyin da mace za ta bi domin naƙaltar sirrin madafinta, yadda za ta faranta wa maigidanta kuma ita ma ta samu rabauta da falalar da ake samu idan an yi biyayyar aure. Mun kawo muku wasu hanyoyi kamar haka:

Kula da irin abincin da ya fi so, kula da lokutan cin abincinsa, kula da lalurarsa ta fuskar cimakar da ta dace, kula da tsaftar madafinki da abinci da sauransu. Inda muka yi muku bayani filla-filla yadda za a gudanar da kowanne daga ciki. Yanzu za mu ci gaba daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. A sha karatu lafiya.

  • Abu na gaba shi ne, tattalin kayan abinci: Ki zama mai tattala wa mai gida kayan abinci idan ya kawo. Kada ki zama mai almubazzaranci mai ɓarnar kayan abinci. A musulunce ma haramun ne. Allah (SWT) ya kira masu varna da ‘yanuwan shaiɗan. Na tabbata wannan ba abinda za ki so a kwatanta ki da shi ba ne. Sannan kuma a wannan yanayin rayuwa da aka tsinci kai ya kamata ki tausaya masa ki dinga tattala abubuwa.

Kada ki dinga dafa abinci ba kai ba gindi yana yawa ana zubarwa. Idan abinci ya yi yawa kamar farar shinkafa ki san dabarar da za ki yi ki sarrafa ta i zuwa wani abu idan ba ki samu almajiri ba kada ki zubar. Haka za ki iya adana miya idan ta yi yawa a firji. Kada ki bar kayan miya ko su dankali ko nama da sauransu su dinga ruvewa a banza. Komai kuɗin namiji yana son a yi masa tattali. Komai ki dinga amfani da dai-dai abinda aka buƙata.

*Abinci mai gina jiki: Ki zama mai samarwa wa iyalanki abinci mai gina jiki. Kada ki zama irin matan da za su kasance masu voye kuɗin cefane a yi wa iyali garau-garau. Hakan yana da illa matuƙa.

*Sarrafa abincin yaranki. Kamar yadda muka sani su yara ƙanana daga wata shidda idan suka fara iya koyon cin abinci akwai ire-iren abinci da ake fara gabatar musu da shi. Misali, kamar abincin gwangwani irin su Cerelac da sauransu. Wasu yaran za a samu ba su son nau’in abincin gwangwani.

Daga nan kuma za mu ce aiki ya same ki matar gida. Domin doke ki ƙoƙarta ki samo wa yaran abinda suke buƙata ta hanyar sarrafa hatsi kamar a yi kamu da sauransu.

Musamamman wanda ya yi shuhra da ake haɗa su dawa da alkama da waken suya da gyaɗa da farar shinkafa a niqo a dinga kamu da shi yana matuƙar ƙara lafiyar yara.

Haka idan aka samu gero ko dawa ko masara zalla su ma ana yi da su, sai dai bai kai wancan na farkon ƙara lafiya ba. Sannan a yi shi cikin tsafta saboda ƙananan yara garkuwar jikinsu tana da rauni. Ba wuya sun ɗauki cuta. Sannan idan yaye za ki yi shi ma kada ki manta yaro yana samun alfanu da garkuwa sosai ta hanyar shan nono.

Idan kika yaye shi ya rasa wannan garkuwa dole sai kin yi ƙoƙari kin samar masa abinci wanda zai ba shi wannan kariya da garkuwa da yake samu daga ruwan nono. Abinci irin su madara, ƙwai, hanta, karas da dafaffen dankalin turawa suna matuƙar taimakawa.

Sannan kuma mata kada mu yi ƙasa a gwiwa ko girman kai ko duhun ka. Ki tsaya ki koyi abinda ba ki iya ba ko ba ki sani ba a dabarun girke-girke da sarrafa abinci. Akwai hanyoyi da dama barkatai. Da ma iyaye mata ya kamata tun kafin ki aurar da ɗiyarki ki koya mata girke-girke da dabarun tsafta da tattali da sauransu.

Su kuma matan aure da ‘yammata da zawarawa ku dinga daurewa kuna shiga azuzuwa na na koyon girki don faɗaɗa iyawarku. Kar ki ce ke komai kin sani. Na tabbata kika shiga sai kin samu abin da ba ki iya ba a baya. Haka a dinga shiga intanet a Youtube ma za ki ga har ma bidiyon yadda ake sarrafa girkin ake nunawa ga shi.

Sannan kar a yi girman kai a, kwantar da kai a koya ko wajen kishiya ne. A gidansu ma kafin ta yi aure ta kula da babarta ko yayarta ta ga yadda suke girki ko maƙwabta ne. Shi ma ilimi ne. Ba wai iyaye ne kaɗai za su dinga qoqarin sai kin koya ba. Duk da dai yana da muhimmancin iyaye su kula da koya wa yara girki.

A nan za mu dakata. Da yardar Allah mai kowa mai komai za mu ci gaba a mako mai zuwa. Allah ya sada mu da alkhairi. Kada a manta a dage da ibada a wannan wata na rahama da jin ƙai. Allah ya sada mu da falalarsa.

Sai wani makon kuma idan mia dukka ya yarje. 08024859793.