Gobara ta laƙume gidaje a Legas

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da aukuwar gobara a wasu jerin gine-gine guda uku kusa da ke Dosumu- Idomota, a yankin Lagos Island a Jihar Legas.

Majiyarmu ta ce gine-ginen da lamarin ya shafa, benaye ne masu hawa uku da huɗu.

Ya zuwa haɗa wannan labari, NEMA ta ce ba a kai ga gano dalilin tashin gobarar ba.

Jami’in NEMA, Ibrahim Farinloye, ya ce hukumar ta fuskantar ƙalubale wajen ƙoƙarin kashe gobarar.

 “Muna fuskantar babban ƙalubale wajen samun ruwan da za a yi amfani da shi wajen kashe gobarar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, motocinsu kan yi tafiya mai nisan gaske kafin ɗauko ruwan da ake amfani da shi wajen kashe wuta.