Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Harkokin Bada Tallafin Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta ci alwashin tallafa wa wasu daga cikin jaruman masana’antar Kannywood da ke fama da rashin lafiya na musamman, a wani yunƙuri na kula da lamuransu.
Babbar Sakatariyar KSCHMA, Hajiya Rahina ta bayyana haka a wani taro da ya haɗa da wakilan Kannywood, hukumar tace finafinai ta jihar da wasu ɓangarori a ofishinta.
A wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN), Shehu Hassan Kano ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an yi haka ne bisa la’akari da taimako da wasu marasa lafiya na cikin Kannywood ke buƙata akan cutukan da ke damun su musamman waɗanda nasu suka fi ƙarfin su kula da su.
A cewarsa, tuni KSCHMA ta fara kulawa da wasu daga ciki waɗanda suka haɗa da Aminun Mahiru, Haruna Titiɓiri, Ladidi Fagge, Abubakar Hunter, Mustapha Musty, Zainab Golden da kuma Zakiyya Ibrahim.
Ya bayyana cewa, an ba kowane mara lafiya da ya halarci zaman fom domin cikewa tare ambatar asibitin da yake son zuwa ana duba shi, yana mai cewa al’amarin ya shafi dukkan wani ɗan Kannywood da ke buƙatar tallafin.
Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban hukumar tace finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha ya kai koken al’amarin zuwa KSCHMA.
Haka kuma, an sanya wa tsarin tallafin suna “Kannywood Abba Healthcare”, yana mai cewa za a sanar da ranar da za kai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ziyarar jinina akan lamarin.
Sauran waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da ƙungiyoyin Arewa Elders, KAFIGAN da wasu jaruman Kannywood.
A ƙarshe, Shehu Hassan Kano ya miƙa godiya a madadin MOPPAN ga Abba El-Mustapha bisa wannan hoɓɓasa wajen ganin an tallafa wa marasa ƙarfi a Kannywood da sauran harkokin ciyar da masana’antar gaba.
