An yi kira ga attajiran Katsina su yi koyi da Lado Ɗanmarke wajen tallafa wa ilimi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗaliban manyan makarantun Jihar Katsina da na wasu a jihohin Kano da Kaduna sun yi kira ga attajirai da manyan kamfanoni da su yi koyi da Sanata Yakubu Lado Danmarke wajen tallafa wa ilimi a Jihar Katsina.

Sanata Ɗanmarke ya kafa gidauniyar ta tallafin karatu da ta daɗe yana tallafa wa karatun ɗaliban Jihar Katsina masu karatu a manyan makarantu da jami’o’in ƙasar nan.

Ya zuwa yanzu ɗalibai 31,711 suka ci gajiyar fiye da Naira miliyan 700 a matsayin tallafin karatu a manyan makarantu da suka haɗa da ABU Zaria,BUK Kano,UMYUK Katsina, FCE Kano,FCE Zaria,UDUS Sokoto,FUDMA Dutsinma da sauran su.

Wasu daga cikin ɗaliban da suka gana da manema labarai a cibiyar koyon sana’o’i ( Katsina Vocational Center) katsina, sun bayyana ilimi a matsayin hasken rayuwa a cewar su kamar yadda wani tsohon gwamnan Jihar Katsina ya taɓa cewa “Hatta haukan mai ilimi ya fi na jahili.”ɗaliban suka ce.

Saratu Lawal Maska wanda ta yi jawabin a madadin ɗaliban sun nuna takaicin su yadda yake neman gagaran talaka saboda tsadar kuɗin makaranta.

“Kuɗin gudanarwa da ciyarwa,samun ilimi ga ya’yan talaka ya ƙara zama tamkar zinariya da lu’ulu “u” a cewar su.

A dai dai wannan lokaci na halin ƙuncin rayuwa wani bawan Allah,ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa mai kishin al’umma a Jihar Sanata Yakubu Lado Danmarke bai gajiya ba wajen cigaba da tallafa wa ɗaliban manyan makarantu ta hanyar biya masu kuɗin makaranta ta hanyar gidauniyar sa.

Ɗaliban sun ƙara kira ga attajirai da manyan kamfanoni da manyan jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su yi koyi da wannan bawan Allah Sanata Lado Danmarke domin ɗan talaka ya sami damar cimma burinsa na samun ilimin zamani da na addini.

Sun bayyana matsalolin sufuri da mayan makarantu da suka haɗa jami’o’in Aƙalam,FUDMA, UMYUK ke fuskanta a kullum wanda shima yana buƙatar kulawar gaggawa.

By ukarofi

Leave a Reply