
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun haɗaka (JTF) a Arewa maso Gabas a ƙarƙashin rundunar Atisayen Haɗin Kai (OPHK), sun yi nasarar ceto mutane 360 da aka yi awon-gaba da su daga komar ƙungiyar Jama’atu Ahlis-Sunna Lidda’Awati wal-Jihad (JAS) a yankin tsaunukan Mandara da ke kudancin Jihar Borno.
Rundunar Sojoji ta bayyana atisayen ceton a matsayin ɗaya daga cikin mafi nasara da aka gudanar a kwanan nan a Nijeriya.
Jami’in hulɗa da jama’a na OPHK, Laftanal Kanal Haruna M. Sani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.
A cewarsa, an ƙaddamar da atisayen ne bayan ɗaukar tsawon makonni ana tara bayanan sirri, lamarin da ya taimaka wa dakarun ceto maza, mata da yara da suka jima a hannu ‘yan ta’adda cikin ƙoshin lafiya. An yi garkuwa da su daga ƙauyuka da dama musamman a yankin Ngoshe.
Laftanal Kanal Sani ya bayyana cewa, an fara tsara atisayen ne a lokacin da aka samu bayanan sirri daga majiyoyi daban-daban da ke nuna ainihin wuraren da waɗanda aka sacen suke.
Akan haka ne dakarun OPHK na sashe na 1 suka yi amfani da salon ƙwarewar aiki wajen tabbatar da cimma nasara akan ‘yan ta’addan, sannan suka ƙaddamar da atisayen, lamarin da ya bayar da damar ceto mutanen.
Babbar Rundunar Sojin Nijeriya ta yaba wa ƙwarin-gwiwa, ƙwarewa da kuma horon dakarun da suka aiwatar da atisayen musamman bisa ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya.
Ta tabbatar wa al’umma cewa za su cigaba da ƙoƙarin ganin an daƙile ayyukan ta’addanci da shafe ‘yan ta’adda, da kariya ga yunƙurin garkuwa a nan gaba gami da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a shiyya da ma ƙasa baki ɗaya.
A wani ɓangare kuwa, Ƙungiyar Haɗakar Matasan Borno ta Kudu (BOSYA) ta tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa baki ɗaya waɗanda aka sace a Ngoshe sun shaƙi iskar ‘yanci a ranar Asabar.
Shugaban BOSYA, Ibrahim Kaigama ya bayyana cewa jarirai huɗu da aka haifa a komar ‘yan ta’addan sun rasu sakamakon cutukan sanyi, inda a yanzu iyayensu na halin karɓar magani a asibitin gwamnati a jihar.
