
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Ƙasa (NARD), ta ba Gwamnatin Tarayya sati uku na ta ɗauki matakan gaggawa wajen daƙile cin zarafi da hare-haren da ake kai wa ma’aikatan lafiya a Nijeriya.
NARD ta bakin Shugabanta, Mohammed Suleiman ta ce cigaba da kai farmaki akan ma’aikatan lafiya barazana ne ga fannin a Nijeriya, don haka nemi gwamnatin da ta ɗauki matakin gaggawa.
A cewarsa, NARD za ta ayyana tsunduma yajin kan rikicinta da gwamnati akan buƙatu guda 14 da ke damun fannin lafiya, inda ya yi gargaɗin cewa rashin magance matsalar akan lokaci ka iya sa a sake shiga yajin aikin.
NARD ta bayyana cewa, aƙalla cibiyoyin lafiya 17 ne suka fuskanci hare-hare cikin shekara guda da ta gabata, inda likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya suka gamu da raunuka da asarar dukiyoyi.
Ta kuma ce, sama da kashi 90 cikin 100 na waɗanda abin ya shafa mambobinta ne, tana mai nuna damuwa kan yadda hare-haren ke ƙaruwa ba tare da an hukunta masu laifi yadda ya kamata ba.
Ƙungiyar ta koka da cewa galibin masu aikata irin waɗannan laifuka na tsallake hukunci, yayin da waɗanda abin ya shafa ke karɓar wasiƙun neman afuwa kawai maimakon ganin an gurfanar da masu laifin a gaban kotu.
Akan haka ne ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar da tsaron ma’aikatan lafiya da wuraren kiwon lafiya, tana mai gargadin cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba, hakan na iya shafar ayyukan kiwon lafiya a faɗin ƙasar.
