Yadda ƙarancin kuɗin Babban Masallacin Ilorin ke jan hankalin duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da Babban Masallacin Juma’a ta birnin Ilorin mai darajar miliyoyin Naira ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin wuraren da suka fi jan hankalin masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya, batun yadda za a ci gaba da kula da wannan gagarumin gini ya fara zama abin damuwa ga masu ruwa da tsaki.

A cikin makonni biyu da suka gabata, shugabannin da ke kula da masallacin sun bayyana damuwarsu kan ƙarancin kuɗaɗen da ake samu domin kula da ginin, wanda ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin mafiya kyau a Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya.

Rahotanni sun nuna cewa masallacin da ke kasuwar Oja-Oba, ɗaura da Fadar Sarkin Ilorin, ya zama wata sabuwar cibiyar yawon buɗe ido, inda baƙi daga ƙasashe irin su Sifaniya, Amurka, Saudiyya, Masar da Belgium ke kai ziyara domin ganin kyawun ginin.

A yayin da ya ke jawabi a taron shekara-shekara na Kwamitin Amintattu da masu ruwa da tsaki na Babbar Masallacin Juma’a ta Ilorin, Shugaban Kwamitin Amintattu, Mai Shari’a Salihu Alfa Belgore (mai ritaya), ya nuna damuwa kan ƙarancin tallafin kuɗi da ake samu domin kula da masallacin.

Ya ce, babu shakka masallacin na daga cikin mafiya kyau a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, yana mai jaddada cewa ci gaba da kula da wannan matsayi na buƙatar kulawa da gyare-gyare akai-akai.

“Har yanzu muna dogaro sosai ne da gudunmawar ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni wajen kula da wannan gini mai daraja,” inji Belgore.

Tsohon Babban Alƙalin Alƙalan Nijeriya ya ƙara da cewa masallacin ba ya samun wata gudunmawar dindindin daga gwamnati, sai dai taimakon da ake samu daga ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa Daular Ilorin.

Ya ce, baya ga hakan, masallacin na rayuwa ne bisa tallafin al’umma da ƙungiyoyi daban-daban, yana mai kira ga masu hannu da shuni da su ƙara bayar da gudunmawa domin tabbatar da ɗorewar ginin.

A nasa jawabin, Sakataren Kwamitin Amintattu kuma Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Tsakiya, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya bayyana cewa an samu ƙarin tallafin kuɗi idan aka kwatanta da shekarun baya.

Ya ce, duk da haka, ana buƙatar kimanin naira miliyan 150 domin gudanar da ayyukan kulawa da samar da wasu muhimman kayayyakin more rayuwa a sabuwar masallacin da kuma tsohuwar Babbar Masallacin Juma’a da ke Idi-Ape a Ilorin.

A cewarsa, jimillar gudummawar da aka samu ta kai naira miliyan 79.7, idan aka kwatanta da kusan naira miliyan 62 da aka samu a shekarar 2021 zuwa 2022.

AbdulGafar, wanda tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kwara ne, ya yi kira ga attajiran Musulmi da su bayar da gudunmawa domin tabbatar da ɗorewar kula da masallacin.

Ya bayyana cewa, kula da gine-ginen masallacin, samar da wutar lantarki da ruwa ba tare da katsewa ba na daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta.

Ya kuma yi gargaɗin cewa ci gaba da dogaro da gudummawar mutane kaɗan ba zai iya ɗorewa ba, yana mai cewa lokaci ya yi da za a samar da tsare-tsaren saka hannun jari masu ɗorewa domin kula da masallacin a nan gaba.

A wani ci gaba kuma, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya ƙaddamar da sabon ginin gudanarwa na Babbar Masallacin Juma’a ta Ilorin.

An kashe kusan Naira miliyan 43 wajen gina wannan gini, wanda zai kasance a matsayin sakatariyar masallacin.

Bayan ƙaddamar da ginin, Sarkin ya yi kira da a yi amfani da shi yadda ya kamata, tare da yabawa Kwamitin Gudanarwar Masallacin bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kula da wannan muhimmiyar cibiyar addini.

A nasa jawabin, Alhaji Shehu AbdulGafar ya bayyana cewa sabon ginin ya ƙunshi ofisoshin sakataren zartarwa, ma’aikatan gudanarwa da kuma babban ɗakin taro na zamani.

Ya ce, an kammala aikin ne ta hanyar amfani da ma’aikata kai tsaye domin rage kuɗin aiki, lamarin da ya sa aka kashe naira miliyan 43 maimakon naira miliyan 57 da aka fara ƙiyasta.

AbdulGafar ya bayyana farin cikinsa da cewa kammala wannan sakatariya ya cika babban tsarin gina harabar masallacin gaba ɗaya.

Ya kuma sake kira ga attajiran ’yan asalin Ilorin da su tallafa da kuɗaɗe domin kula da masallacin, wanda ya ce kyawunsa da tsarinsa na ci gaba da jawo baƙi daga ƙasashe daban-daban na duniya zuwa Ilorin.

By ukarofi

Leave a Reply