An gudanar da jana’izar wani ɗan Nijeriya kuma babban masoyin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, bayan da rahotanni suka bayyana cewa ya rasu yayin da yake kallon wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai ta UEFA tsakanin Arsenal da Paris Saint-Germain (PSG).
Marigayin mai suna Chibuzor Nzediegwu, ɗan garin Uga da ke ƙaramar Hukumar Aguata a Jihar Anambra, an ce ya faɗi sumamme ne yayin da wasan ke gudana bayan PSG ta farke ƙwallon da Arsenal ta ci, lamarin da ya ƙara zafafa fafatawar tare da matsa lamba ga magoya bayan Arsenal.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a rabin lokaci na biyu na wasan, wanda daga bisani ya ƙare da takaici ga magoya bayan Arsenal bayan PSG ta lashe kambun Gasar Zakarun Turai ta shekarar 2026.
Rasuwar tasa ta jefa iyalansa da al’ummarsa cikin alhini, inda aka ga ’yan uwa da mazauna yankin sun hallara domin gudanar da jana’izarsa tare da wasu al’adun gargajiya kafin a binne shi.
Mutane da dama sun bayyana marigayin a matsayin mai matuƙar son ƙwallon ƙafa, kuma rahotanni sun ce ya shiga cikin matsanancin damuwa yayin wasan kafin ya yanke jiki ya faɗi, lamarin da ya tayar da martani da tausayawa a kafafen sada zumunta.
Wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai ta 2026 da aka buga a filin wasan Puskas Arena da ke Budapest na ƙasar Hungary a ranar 30 ga Mayu, ya ƙare da ci 1-1 bayan ƙarin lokaci. Daga bisani PSG ta doke Arsenal da ci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Yayin da ake ci gaba da aika saƙonnin ta’aziyya, lamarin ya sake haifar da muhawara kan tasirin matsanancin damuwa da tashin hankali ga lafiya, musamman a lokacin manyan wasannin ƙwallon ƙafa da ke ɗaukar hankalin magoya baya.
Sai dai babu wata sanarwa daga hukumomin lafiya da ta tabbatar da ainihin musabbabin rasuwar marigayin, duk da cewa mutane da dama sun danganta lamarin da matsanancin tashin hankali da ya biyo bayan wasan.
