Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Barka da safiya malama Aisha. Na san ba ki san ko wacce ce ni ba, sunana…………kuma na samu number ki ta hannun Hajiya…………ƙawata ce, lokacin da na ke mata bayanin halin da nake ciki ne, sai ta ce, ga number na kira ki, ke ce wadda ki ka zo har gida lokacin da matsalarta da……………..ta yi tsanani, ke ki ka taimaka har aka samu mafita.

Malama Aisha, mijina ne can baya shekaru da yawa, shi da wani wan babanshi suka shigo da yamma, wan baban nasa ɗauke da jinjiri, suka ce a Masallacin unguwar wan baban ne aka ajiye shi, ba a san waye ya ajiye ba. Shi ne wan baban ya ba wa mijina shawarar me zai hana ya ɗauka ya riqe tunda mu ba mu sami haihuwa ba. Shi ne mijin nawa ya ce sai dai idan na aminta da hakan. Na karɓi yaron na riƙe, shi kuma maigidana ya siyo duk abinda ya kamata muka kula da jinjirin.

Shekaru biyu bayan nan na samu haihuwa ni ma dai namiji. Na haɗa su su biyu. Ban tava nuna bambanci a tsakanin su ba. Shekaru huɗu bayan haka, maigidana ya qara dawowa tare da limamin unguwarmu tun da asubahin, limamin na san shi sosai don shi ke wa’azi duk bayan magariba zuwa Isha’i. Hannunshi ɗauke da wani jinjiri, wai an ajiye shi a Masallaci kafin a yi kira, ko da ya shigo ya same shi a ciki. Shi ne ya nemi maigidana tunda ya ji labarin yadda ya yi aikin Allah a wancan karo, ko za mu ƙara da wannan. Anan ya dinga yi min wa’azi da nunamin falalar renon jinjirin, har sai da na ji jikina ya yi sanyi, na amince na karve shi matsayin ɗana na uku.

Yanzu yaran sun girma, sai kuma ‘yan surutai suka fara tashi na kamar da yaran ke yi da juna, kuma wai suna kama da maigidana, tun ina musanta abin, har zuciyata ta fara yi min kwashe-kwashe, har ni ma na fara hango kamar.

Ds abin ya yi yawa ne, sai na fara tunanin fitar da kaina daga tunanin. Ranar muna kwance a ɗaki, na cewa maigidana, ɗazu mun yi baƙi da bayanan, kamar na kira shi a waya, tsabar ruxewa ya sa ban kira ba. Na ce masa wata mata ce da mijinta suka zo wai babban yaron, sunansa…………….ɗansu ne. wallahi malama Aisha sai kinga yadda ya ruɗe, ya tashi cikin firgici, bai tsaya jin komai ba ya dinga ƙaryata su. Ya sa kayanshi ya fice daga gidan, bai dawo ba sai 12.

Akan wannan maganar sai da aka yi wata bai dawo hayyacinsa ba. Kullum zancen ɗaya ne, hakan sai ya qara min zarginsa. Ki ba ni shawarar yadda zan bi da lamarin, ta yadda ba zan yi nadama ba. {Saƙon ya zo ta murya ne, don haka ya yi tsayi sosai, hakan ya sa dole muka katse wasu batutuwa}.

AMSA:

Anan ‘yar uwa kina da zaɓi da yawa, sai dai tunda kin fara hawa kan wata hanyar ƙarasa ta ma kawai zai iya bada mafita, wato ci gaba da wasan kwaikwayon da ki ka fara shiryawa mijin, tunda kin lura da alamun rashin gaskiya da ki ka yi ma shi hakan.

Za ki iya neman wani ko wata daga ‘yan uwan ƙawayenki ko waɗanda ba a san su ba, su zo don tabbatar da zancen da ki ka yi, wato dai iyayen yaron naku. Ta nan ma za ki iya gane wasu abubuwa, musamman ma idan sun tsaya tsayin daka cewa yaron nasu ne, da hujjar hotunsa yana jinjiri da ma wasu ababe da suka shafi jarintakarshi kafin a kawo maku shi. Sai dai wannan hanyar za ta iya kwaɓewa, kuma zata iya ɗaukar tsayin lokaci ba ta yi tasiri ba. Don haka nake ganin hanya ta biyu ce mafi sauƙi da dacewa, matsalarta kawai idan akwai rashin kuɗi a tare da ke.

Ba kowacce ba ce face gwaji a asibiti don gane idan ɗiyan na mijinki ne, sai dai gwajin da zai ba ki tabbaci na lokaci ɗaya, wato DNA test yana da ɗan kuɗi kamar yadda na ji. Idan babu matsalar kuɗin, sai ki duba daga cikin yaran wane ya fi kama da shi ta halitta, kamar ido, hanci, ƙafa da sauransu. Ba kama ta ɗabi’a ba, sai ki yi gwajin kansa. Samun abinda za ki yi gwajin mai sauqi ne, don za ki iya amfani da abin goge bakin mijinki da na yaron, ko buroshin taje kai da sauran ababen da zai iya ɗaukar ƙwayoyin da za a gwada ɗin. Za ki iya yin wannan gwajin ba tare da kowa ya sani ba.

Kinga idan zarginki gaskiya ne to fa za ki samu hujja mai ƙarfi da za ki iya tunkarar mijinki da ita, kuma ba shi da bakin kare kansa tunda ya san kina da hujja. Idan kuwa yaye-yayen shaiɗan ne kinga kin kawar da shi, kin samu natsu, kuma ba ki jefi mijinki da mummanar kalma ba.

Hanyoyin na da yawa, sai dai lokaci ba zai ba mu damar zayyano su ɗaya bayan ɗaya ba, sai dai ina da tabbacin da za ki samu yin shawarar ta biyu, duk matsalar za ta zo da sauƙi ƙwarai. Sai dai kamar yadda na faɗa a baya, duk yadda lamarin ya kasance ke ce da riba, domin kin riqe yaran da uwarsu ta ƙi kula da su, kuma kin riƙe su tsakani da Allah, don haka sakamakon ki babba ne a wurin mai bayyar da babban rabo.

Zancen hukuncin da za ki iya ɗauka idan ki ka gano yaran na mijinki ne kuwa, yana hannunki, duk da cewa mijinki ya ha’ince ki, ya rufe ki kan abinda idan kin sani ba za ki aminta da shi ba, wanna kuma zalunci ne, hakan ba yana nufin Musulunci ya raba aurenku ba, ko ya yanke hukunci kai tsaye kan wannan lamari ba. Saidai shawarata ki ba shi dama ki ji ta bakinshi, ma’ana kada ki yanke hukunci cikin fushi.

Idan ya ba ki hujjar da ki ka gamsu, babu laifi don kin yi haƙuri, kin karɓi jarrabawar da Allah Ya yi miki, kin rungumi qaddara, kin ci gaba da riqe yaran waɗanda babu laifinsu a ciki, don su ma sun ta shi ne suka gansu a ciki.

Idan kuwa kin kasa gamsuwa da hujjar, ko zuciyar ta qi aminta da cin amanar da aka yi maki, to ki zaɓi mafita da ba za ta janyo fushin Allah kanki ba, wato cutar da yaran ko ci gaba da zama da mijin don kawai ki ɗau fansa.

Allah ne mafi sani.