Ningi: Nijeriya iya ruwa fidda kai!

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Na aara yarda da wannan azancin zance na IYA RUWA FIDDA KAI a lamuran Nijeriya. Ga ma wasu kalaman da ke cewa duk wanda ya iya allonsa ya wanke kazalika in ka iya ruwa ka iya laka. In mun tuna lokacin da tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta bullo da shirin ba da lada ga masu kwarmato an samu waɗanda su ka yi yunƙurin zama ‘yan kwarmaton.

A iya sani na akwai wadanda su ka samu matala a wajen aikin su don maimakon su samu la’ada sai su ka samu kasadar ɗaure su ko ma zama su ne abun tuhuma. Waɗanda ke waje da gwamnati kan iya ba da irin wannan labari da aƙalla dai sun furta ko ba la’ada sa samu ladar yabo daga mutane. Kazalika wannan ba ya na nuna masu kwarmato daidai su ke yi ko labarin su 100% gaskiya ba ne. Wani abun kuma shi ne duk wanda ke gidan gilashi ya guji wasan jifa don zai fi kowa asara.

Face mutum zai yi kasadar wakar marigayi Mamman Shata ta Umaru Ɗan Ɗan Duna Gwandu inda ya ke cewa sai in daji ya yi dameji ne Umaru kan je ya dubo “JIRGI YA NIKE HANYAR MAZA KU BI BAYA” in mutum zai zama kwamandan aukawa kasada sai ya shirya duk yadda ta kaya ba shi da nadamar sakamakon matakin da ya ɗauka.

Tsari ne da ke cike da kwane-kwane da dabaru da sai mutum ya yi dogon nazari kafin cimma gaci ba tare da targaɗe ba. Yayin da mulkin soja ke zama ba tare da tsarin mulki ba kazalika ba bambancin jam’iyyar siyasa; mulkin dimokraɗiyya na da dukkan waxannan abubuwan biyu. Wannan gwamnati ta Bola Tinubu ma ba ta samu yadda ta ke so ba ne tun da ta gaji mulki daga jam’iyyar ta ta APC ne don haka caccakar gwamnatin baya ko da an samu matsaloli sai a na sara a na duba bakin gatari.

Ai lokacin da Buhari ya shigo mulki a 2015 ya yi ta maganar yadda PDP ta lalata ƙasa a tsawon shekaru 16 daga 1999-2015. Ita kuma gwamnatin Tinubu ba zai zama da tunani ta cigaba da kushe PDP ba don tuni jam’iyyar ta APC ta share shekaru 8 kan mulki da ya dace a ce ta gyara lamura. Mun dan ji gwamnatin ta Tinubu ta fara caccakar tsohuwar gwamnatin Buhari amma hakan ya dakata in ka ɗebe batun tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele.

Jama’a na muhawara kan dalilan da su ka saka majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku biyo bayan kalamai kan zargin kumbiya-kumbiya a kasafin kuɗin bana 2024.

Duk da Sanata Ningi ya yi kandagarki na nuna an sauya ma sa kalamai kan zargin amfani da kasafi biyu; hakan bai hana majalisar qarqashin Godswill Akpabio ta dakatar da shi ba.

Kazalika ba tabbacin ko Ningi zai rubuta takardar neman afuwa don duba janye dakatarwar bisa buƙatar majalisar.

Mutane na ganin zai yi wuya mai kwarmato a cikin majalisa ko gwamnati ya iya kai labari ba tare da an dau matakin aware a kan sa ba.

Ba wannan ne karo na farko majalisar dokokin Njeriya ke dakatar da ɗan majalisa ba bisa ayyukan da su ka ci karo da muradun majalisar ba.

Sanata Abdul Ningi daga Buachi ta tsakiya ya ce sam bai zargi shugaba Tinubu da aiwatar da kasafin kuɗi kala biyu ba.

Ningi wanda ke jagorantar zauren ‘yan majalisa na arewa ya ce ba inda ya furta cewa Tinubu na amfani da kasafi mai Naira tiriliyan 25 da mai Naira tiriliyan 28.

Kazalika Ningi ya ce batun da ya yi ma da ya ce an juya ba ya yi a matsayin shugaban zauren ‘yan majalisa na arewa ba ne amma ya yi hakan a kashin kan sa ne.

Gabanin nan fadar shugaban ƙasa ASO ROCK ta nuna takaici kan kalaman da ta ce sun fito ne ma daga babban dan majalisa.

Wannan ya nuna Abdul Ningi ta kan yiwu ya hango abun da zai iya faruwa daga irin kalamai masu kama da hakan da su ka kai ga babban mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan sadarwa Bayo Onanuga maida martani mai zafi. Duk ƙoƙarin ƙarin bayani bai sa majalisar ta gamsu ta dakatar da ɗaukar matakin mai zafi kan Ningi ba.

Gabanin nan ma dama ƙungiyar ‘yan majalisar na arewa da Abdul Ningi ke jagoranta ta titsiye shugaban majalisar kan zargin wariya a kasafin na 2024.

‘Yan majalisar dattawa na yankin arewacin Nijeriya sun titsiye shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio kan bahasin ƙara Naira tiriliyan 4 a wasu ayyuka a kasafin 2024.

Tuni dai an fara aiki da kasafin da ya zama ya kan fara aiki daga watan Janairu zuwa Disamba.

A ganawa a masaukin baƙin shugaban majalisar a Asokoro Abuja, ‘yan majalisar qarqashin Sanata Abdul Ningi sun ce an cusa voyayyun aiyuka na waɗannan maqudan kudin cikin kasafin don amfanin ‘yan lelen shugaban majalisar.

Kazalika ‘yan majalisar sun ce an yi wa yankin Arewa da wani sashe na kudu kwange a kasafin.

Bayanan sun nuna Akpabio bai musanta cusa kuɗin ba amma ya ce an yi hakanne a lokacin ya na kwance a asibiti.

Jerin matakan da ya zama Ningi na ciki zai sa a ɗau mataki a kan sa don aƙalla a rage ma sa gudu a gwamnatin da alamu ke nuna kowa ta sa ta fishshe shi. Ai yanzu wasu manyan ’yan siyasar ƙasar nan na neman hanyar tasiri ne a gwamnatin taraiya ba wajen jam’iyyar su ko jama’arsu ba. Ma’ana wani abun ya wuce a tuna akwai APC, PDP da sauran jam’iyyu da ke da wakilci a majalisa.

Abun da za mu yi fata shi ne talakawa su samu sauƙin rayuwa da cushe a kasafi ko da tsumbure. Duk matakin da za a ɗauka in ba zai rage wannan ƙunci mai tsanani ba to aikin baban-giwa ne.

Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta bayyana cewa a watan Janairun bana 2024 matsakaicin abinci mai ma’ana da zai wadaci mutum ɗaya ya kai Naira 858.

Hukumar ta ce an duba alƙaluman yadda matsakaicin abinci mai amfani a jiki ya ke ne bisa ma’aunin duniya.

NBS ta ƙara da cewa lissafin bai haɗa da kuɗin sufuri ba da ma kuɗin haɗa abincin.

A nan hukumar ƙididdigar ta nuna mafi tsadar abincin a yankin kudu maso yamma ne inda kudu maso gabar ke biye yayin da arewa maso yamma ke da mafi sauƙi.

An ga bayyanar dogayen layukan neman mai a kusan dukkan gidajen mai a Abuja da hakan ke nuna fargabar tashin farashi.

Lamarin ya afku ba tare da wata sanarwa ko ankararwa cewa za a samu ƙarancin man ba.

Wasu gidajen man ma a rufe su ke yayin da matasa masu jarka su ka buɗe kasuwar su a gefen titi.

Haƙiƙa farashin man ya doshi Naira 700 amma wasu na sayarwa kimanin Naira 650 zuwa sama.

Dama lamarin farashin mai ya zama a hannun ‘yan kasuwa da kan tada farashin lokacin da su ka ga ya dace su yi hakan don samun riba.

Kamfanin mai na NNPCL ya ce ba buƙatar firgita don akwai wadataccen man da zai ishi jama’a.

Yayin da wannan ke faruwa mai bincike na hukumar yaqi da cin hanci ta ICPC Agboro Micheal ya shaidawa babbar kotun Abuja cewa tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya ba wa matar sa da wata ma’aikaciyar bankin Sa’adatu Yaro kwangila mai tsoka.

Wannan na daga tuhumar da a ke yi wa Emefiele kan amfani da muƙamin sa wajen karkatar da dukiyar gwamnati don muradun kashin kai.

Emeiele wanda tsohon shugaba Jonathan ya nada, ya samu dama shugaba Buhari ya bar shi a kujerar har ya kammala wa’adi a bara inda shugaba mai ci Bola Tinubu ya kwave shi a watan Yunin barar.

Yanzu dai an daidaita cajin da a ke yi wa tsohon gwamnan bankin zuwa 20.

Emefiele na maimaita cewa bai aikata laifi ba.

Ba mamaki wannan na daga matakan motsi ya fi lavewa daga hukumomin yaqi da almundahana.

kammalawa;

Nijeriya ce mafi girman ƙasashe da ke yawan baqar fata a duniya kuma a yanzu ta na xaya daga cikin ƙasashe masu saurin samun ƙarin yawan mutane. Ga arziki a ƙasar ta sama da kasa amma har yanzu gajiyar ba ta kai ga akasarin jama’a da ke zama talakawa da ba sa iya samun abinci sau uku a wuni. Wace gwamnati ce za ta gano bakin zaren da mutane za su sarara su daina hamma da ƙorafi? Wannan babban qalubale ga hukumomi su sani alkawarin da su ke xauka na kamfen na kawo gyara ba abun da za a manta da shi ba ne.

Ya kamata a nemo ƙwararru a kowane vangaren gwamnati don gano yanda idan rijiyar Nijeriya ta kawo ruwa to guga ba za ta hana ba. Mu na addu’ar Allah ya sa mu na raye mu ga wanda zai yi wa talakawa adalci ta hanyar samun sauqin rayuwa.