Hedikwatar Tsaro na shirin fitar da sunayen ‘yan ta’addan da take nema ruwa a jallo

Daga BASHIR ISAH

Alamu na nuni da cewa nan ba da daɗewa ba, Babban Ofishin Tsaro zai saki sunaye da hotunan kwamandojin ‘yan fashin dajin da ake nema ruwa a jallo a sassan Nijeriya.

Majiyarmu ta tattaro cewar, rundunar soji ta ɗauki matakin yin haka ne biyo bayan bayyanar wasu sabbin shugabannin ‘yan ta’addan sakamakon kakkaɓe na da da aka yi.

Idan za a iya tunawa, a watan Nuwamban 2022 Babban Ofishin Tsaro ya sanar kan cewa yana neman wasu kwamandojin ‘yan ta’addan aƙalla su 19 ruwa a jallo, tare da sanya tukwicin Naira milyan 5 a kan kowannensu ga duk wanda ya ba da bayanin inda za a same su.

Daga cikin ‘yan ta’addan da aka ba dada cigiyarsu a wancan karon har da Bello Turji daga ƙauyen Fakai a Jihar Zamfara; Ali Kachalla wanda aka fi sani da Ali Kawaje, daga ƙauyen Kuyambara a yankin Ƙaramar Hukumar Danaadau Maru, Jihar Zamfara; Ado Aliero, daga ƙauyen Yankuzo a Ƙaramar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara; Halilu Sububu daga ƙauyen Sububu a Ƙaramar Hukumar Maradun, Zamfara.

Sauran su ne, Sani Dangote daga ƙauyen Dumbarum a Ƙaramar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara; Leko (ƙauyen Mozoj, Ƙaramar Hukumar Mutazu, Jihar Katsina); Dogo Nahali (ƙauyenbYar Tsamiyar Jno a Ƙaramar Hukumar Kankara, Jihar Katsina); Nagona daga Angwan Galadima a Ƙaramar Hukumar Isa, Jihar Sokoto.

Monore daga Yantumaki a Ƙaramar Hukumar Dan, Jihar Katsina; Gwaska Dankarami daga Shamushele a Ƙaramar Hukumar Zuri, Jihar Zamfara; Baleri Ƙaramar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara sai kuma Mamudu Tainange daga ƙauyenb Varanda a Ƙaramar Hukumar Batsari, Jihar Katsina da dau sauransu.

Wata majiya ta ce rundunar soji na shirin fitar da sabbin sunayen gaggan ‘yan fashin dajin da take nema ruwa a jallo a wannan karon.

“Muna kira ga ‘yan Nijeriya da su ba haɗin kawai domin kakkaɓe su kamar yadda suka bada haɗin kai a baya,” in ji majiyar.