Allah Ya yi wa Sheikh Surajo Rabi’ah rasuwa

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa fitaccen malamin nan, Sheikh Surajo Rabi’ah, rasuwa a Gusau, babban Jihar Zamfara.

Da ƙarfe 6 na yammacin Lahadi ake sa ran za a yi jana’izar marigayin a Masallacin Rabi’ah, inda jama’a za su haɗu don gabatar da sallar janaza.

Kawo yanzu, jama’a da dama kuma daga sassa daban-daban ke ci gaba da miƙa saƙonnin ta’aziyya tare da taya ‘yan marigayin alhinin wannan rashi.

A halin rayuwarsa, marigayin ya yi fice wajen yin da’awa ƙarƙashin Ƙungiyar Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatus Sunna.