Kamar yadda aka sani ne, Allah ya kawo mu watan Ramadana mai albarka, wanda a cikinsa ake gudanar da ibadu masu ninkin lada, waɗanda idan mutum ya aikata su zai kasance yana da lada mai tarin yawan da ya fi waɗanda ya yi in ba a watan ba ne, kamar dai yadda malamai masana ba su ƙasa a gwiwa ba a duk lokacin da watan shigo.
Shi watan Ramadan wata ne wanda Allah ya wajabta a yi azumi a cikinsa, sannan aka wajabta wasu abubuwa da dama, aka kuma haramta wasu abubuwan da ba haramun ba ne a watan da ba shi ba, sannan kuma aka ƙara haramta wasu abubuwan da a da ma suke haramun.
Daidai gwarwado za mu ɗan yi bayani game da wasu abubuwa da shi wannan wata mai alfarma ya ƙunsa, waɗanda idan mutum ya kiyaye su zai zama yana daga cikin ’yantattun bayi, waɗanda Allah ke farin ciki da su. Sannan kuma akwai abubuwan ƙyama, kamar dai yadda na ambata a baya.
Masana kiwon lafiya kuma sun bayyana cewa shi Azumi yana da matuƙar amfani a jikin ɗan adam. Don haka yana da muhimmanci mutum ya kasance yana sane da wannan, ya sani cewa bayan ladan da ke cikinsa, akwai kuma wani amfani da yake da shi a jiki. To ballantana kuma a ce a wannan wata mai alfarma.
Idan mutum ya kasance yana azumi, ya zama a kowace daƙiƙa yana cikin lada ne, lokacin yin sahur yana samun lada, barcinsa yana cikin lada, neman abinci mutum na cikin aikin lada, lokacin buɗa baki, kowace loma tana cikin lada, ballantana kuma mutum ya kasance yana cikin ibada, kamar salla ko karatun Alƙur’ani ko sada zuminci.
Ga kowane Musulmi, azumin watan Ramadan wajibi ne, wanda idan mutum ya ƙi yinsa da gangan, to yana cikin fushin Allah har sai ranar da ya gano ya tuba ya kuma rama shi sannan zai kasance tubabbe. Haka kuma akwai matakai na ladabtarwa da addinin musulunci ya tanada ga duk irin waɗannan mutane masu wasa da Azumi.
Sannan kuma, kamar yadda muka faɗa a sama, akwai abubuwa da dama, waɗanda watan Ramadan ke da su, wanda kuma sauran watannin ba su sa da shi. Inda na kawo nunnunka ayyukan alhairi, wanda wannan ne ma ya sa wasu masu hannu da shuni, masu kuma zuciyar bayarwa, waɗanda Allah ya nuna suna da babban rabo, a duk lokacin da wannan wata ya zo sukan kasance suna ciyarwa, musamman ga waɗanda ba su da shi.
Sai dai a wannan harkar ciyarwa da irin waɗannan mutane ke yi, sun rabu kashi biyu ne, wasu na ciyarwar ne ta hanyar sayen ɗanyen abinci su raba ma mutane, wasu kuma sukan dafa ne su rinƙa ba mabuƙata. Wanda ina ganin duk wanda mutum ya yi yana da kyau.
Baya ga ciyarwa da wasu masu kuɗi kan yi daidai gwargwadon ƙarfinsu, wasu kuma ƙaimi suke ƙarawa a harkar ibadar suke yi ta yau da kullum. Wato sukan ƙara a kan nafilfilin da suke yi a kullum, musamman da daddare, su kuma ƙara yawan surorin da suke karantawa a duk rana da dai sauran ibadun da mutum ke gudanarwa a kullum.
Wani abu ga wannan watan shi ne, a duk lokacin da ya shigo sai ka tarar da cewa masallatai na ƙara cika, wuraren alfasha da shaye-shaye suna raguwa, wasu ma rufe su ake yi gaba ɗaya sakamakon tuba da masu aikata irin waɗannan abubuwa suka yi. Wata ƙila ba ya rasa nasaba da batun da Malamai ke cewa ana ɗaure shaiɗanu a duk lokacin wannan wata ya shigo.
Da irin wannan ne ya sa Malaman ke kira ga irin waɗannan mutane da cewa me zai hana su daure su ci gaba da wannan tuba da suka yi ko da watan ya wuce? Saboda wannan yana nuni da cewa ashe dai mutum shi ke da damar ya aikata savo ko kar ya aikata.
Akwai matuqar muhimmanci Musulmi ya sani cewa irin waɗannan abubuwa da ake yi a watan nan, na ƙarin ibadu ne ko daina savo ne, to ya kasance mutum ya ɗore a kai ko da kuwa watan ya wuce ne, domin ta haka ne mutum zai iya samun babban rabon da muka yi magana a sama, haka ne kuma mutum zai samu yin tuba tabbatacciya.
A wannan wata ana buƙatar mutum ya ƙara daga abubuwan da yake yi na ibada da sauran harkokin kyautatawa a tsakaninsa da jama’a, domin ana nunnunkasu ne, savanin sauran watanni. Sannan mutum ya rage daga cikin munanan ayyukan da yake aikatawa, ko ma ya bar su gaba ɗaya.
A wannan wata ana son mutum ya rage fushi, ya rage husuma da jama’a, ya rage barci da daddare, ya rage kalle-kallen da ba za su amfani rayuwarsa ba, ya rage surutu da dai sauran nunanan abubuwan da kowa ya san mummuna ne.
Akwai kuma matuƙar muhimmanci Musulmi ya ƙara a nafilfilinsa, ya ƙara a kan haƙurinsa da duk mutumin da hulɗa da haɗa shi da shi, ya ƙara a sadakokinsa, ya ƙara a kan zumuncinsa, ya ƙara a kan duk wani nau’i na ibada.
Haka kuma kamar yadda na faɗa na sama, masana harkar kiwon lafiya su ma ba a bar su a baya ba wajen bayyana abubuwan da musulmi zai kasance ya lizimta da waɗanda zai guda don samun sauƙin wahalhalun da ce cikin azumin.
Misali, masana harkar lafiyar suna maganar cewa yana da muhimaci idan mutum ya kai azumi ya fara buɗe baki da ruwa mai ɗumi ko wani kayan lambu ko dabino. Suka ce, domin hanji ya riga ya sha wiya ya tsuke, amma idan aka sha abu mai ɗumi zai buɗa shi ya warware ta yadda za a ci abinci mai nauyi ya zauna, kar mutum ya fara buɗe baki da abu mai nauyi.
Haka kuma an yi bayanin cewa a kiyaye kwanciya da zarar an ci abinci, domin yin haka yana da babbar illa ga lafiyar ɗan adam. Akwai bayanai da dama game da wannan azumi mai albarka, waɗanda Malamai da masana kiwon lafiya suka yi magana a kai.
A ƙarshe muna roƙon Allah ya nuna mana farkon wannan wata cikin ƙoshin lafiya da yalwar arziki, ya ba mu ikon nunnunka ayyukan alhairi a cikin wannan wata, ya ba mu ikon guje wa duk wasu munanan ayyuka, sannan Allah ya nuna mana ƙarshensa lafiya cikin ƙoshin lafiya da yalwal arziki, ya nuna mana na shekaru masu yawa.
