Gwamnatin Tarayya ta keɓe Dala Biliyan 1.3 don aikin dogo daga Kano zuwa Nijar

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Sufuri, Said Alkali, ya sanar da wani gagarumin cigaba a fannin samar da kuɗaɗen aikin titin jirgin ƙasa daga Kano-Katsina-Jibiya-Maradi, inda aka samu dala biliyan 1.3 don gudanar da wannan shiri.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin jama’a na ministan, Jamilu Ja’afar ya fitar, an yaba da wannan nasarar a matsayin wani muhimmin mataki na inganta alaƙar zamantakewa da tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

“Dala biliyan 1.3 da aka samu na aikin layin dogo na Kano-Katsina-Jibiya-Maradi babban nasara ne,” inji Alkali.

Manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya Fidet Okhiria da babban darakta a bankin raya ƙasashen Afirka Muhammad Abdulrazak duk sun amince da aikin a matsayin wani abin da zai kawo sauyi mai kyau, da bunqasa tattalin arziki da haɗin gwiwa a yankin.

Ziyarar da Tang Zhigang, shugaban hukumar sa ido ta kamfanin inshorar fitar da kayayyaki da lamuni ta ƙasar Sin, da tawagarsa suka kai a baya bayan nan, ta ƙara sa ƙaimi ga aikin layin dogo na samar da hanyar samun cigaba a tsakanin ƙasashen biyu.

“Layin dogo na Kano-Katsina-Jibiya-Maradi ya nuna tarihinmu da burinmu na cigaban tattalin arziki. Za ta samar da dawwamammen gado na arziki da damarmaki ga Nijeriya da Jamhuriyar Nijar,” inji Alƙali.

Sanarwar ta bayyana ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ganin an samu cigaba da haɗin kai yayin da aikin ke tafiya.

Ma’aikatar Sufuri ta yi alƙawarin samar da sabuntawa aikin akai-akai.

By Editor