‘Yan bindiga a Bauchi sun kashe basarake sa’o’i 24 bayan sun yi garkuwa da shi

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a Jihar Bauchi sun kashe Dagacin ƙauyen Riruwai, Alhaji Garba Bafamasi, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Toro a jihar.

MANHAJA ta kalato cewar, ‘yan ta’addan sun kashe basaraken ne sa’o’i 24 bayan da suka yi garkuwa da shi.

Rahotanni sun ce a ranar Juma’a, 15 ga Maris, ‘yan bindigar suka dira fadar Alhaji Badamasi inda suka razanar da jama’ar yankin da harbin bindiga kafin daga bisani suka yi awon gaba da shi.

Majaiyarmu ta ce, ‘yan bindigar ba su damu da kiran ‘yan basaraken don neman fansa ba, lamarin da ya sa aka kasa gane dalilin da ya sa suka aikata masa haka.

Bayan kwana guda da yin garkuwa da marigayin sai aka tsinci gawarsa a gefen gari kusa da ƙauyen.

An gano gangar jikin ne a lokacin da jama’ar kauyen suka baza neman basaraken a daji.