Gobara ta laƙume wani sashen Babbar Kasuwar Sakkwato

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni da muka samu daga jihar Sakkwato na nuni da cewa, an samu aukuwar gobara a Babbar Kasuwar Sakkwato.

Bayanai sun ce gobarar ta fi ƙamari a sashen masu sayar da bababura a kasuwar.

Duk da dai babu cikakken bayani kan dalilin aukuwar gobarar, sai dai MANHAJA ta tattaro cewar da safiyar ranar Litinin iftila’in ya auku.

Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Babura a Kasuwar, Shehu Muhammad, ya ce ba a kai ga gano adadin ɓarnar da gobarar ta yi ba saboda rashin tsagaitawar wutar.

An ga jami’an kashe gobada na jiha da na tarayya a wurin da gobarar ta auku, inda suke ta yin bakin ƙoƙarinsu wajen kashe wutar.