‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 87 a wani sabon hari a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a Jihar Kaduna sun yi garkuwa da mutum 87 a wani sabon harin da suka kai yankin Tashar Kajuru da ke jihar.

Wani matashi a yankin mai suna Harisu Dari, shi ne ya tabbatar da aukuwar hakan ga majiyarmu a ranar Litinin.

Wannan na zuwa ne bayan wasu ‘yan kwanaki da ‘yan bindigar suka hari a yankin Dogon Noma da kuma kauyen Kuriga inda suka sace ɗailiban firamare su sama da 200.

Bayanai sun ce, maharan sun kuma fasa shaguna inda suka kwashi kayayyaki da dama yayin harin.

Yawan hare-haren ta’addancin da ke aukuwa a yankunan ƙananan hukumomin Kajuru da Chikun sun jema mazauna ya kin cikin halin firgici da ɗarɗar, lamarin da ya sa suke kira ga gwamnati a matakai daban da a hanzarta ɗaukar matakan da suka dace domin maido da salama a yankunan.

Ya zuwa haɗa wannan labari, mazauna yankin da lamarin ya shafa na ci gaba da ƙoƙarin ganin yadda za yi domin isa ga waɗanda aka yi garkuwan da su.